Gwamna Ganduje ya ce ana sakaci da tsaro a iyakokinsu

Gwamna Ganduje ya ce ana sakaci da tsaro a iyakokinsu

Gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano, ya nuna rashin gamsuwa da yadda ake tsare iyakokin jahar sabanin yadda ya yi umurni.

Ganduje ya bayyana cewa direbobin motoci musamman na kasuwa sun gano wasu barayin hanyoyi da suke da suke bi suna shiga jahar ba tare da sanin jami’an tsaro ba.

Ya ce: “A gaskiya ba mu yi amanna da yadda ake tsare iyakokinmu ba musamman na kasa domin ana bari motoci suna shiga jahar ba tare da sun dauko komai ba.”

Gwamna Ganduje ya ce ana sakaci da tsaro a iyakokinsu
Gwamna Ganduje ya ce ana sakaci da tsaro a iyakokinsu
Asali: Twitter

Gwamnan Kanon ya kara da cewa a lokuta mabanbanta direbobi kan ajiye fasinjoji kafin a isa wajen da jami’an tsaro suke, sai fasinjojin su tafi a kafa ko a dauke su a kan babur sai su hade a gaba bayan jami’an tsaro sun duba mota ba kowa.

A cewarsa: “Hakan dabarace saboda haka ba zamu amince da irin haka ba”.

Gwamnan ya bayyana cewa da kansa ya kama wasu mutane da suka so shiga cikin jahar wadanda suka fito daga yankin Madalla na jahar Niger.

KU KARANTA KUMA: Labari da dumi-dumi: Mutum na biyu ya mutu a Najeriya sakamakon Coronavirus

Ganduje ya ce muddin ana bari irin wadannan mutane da suka fito daga wasu wurare musamman inda aka samu bullsr Coronavirus suna shiga dashi cikin jahar, shakka babu za a iya kai musu cutar.

A wani labarin kuma, mun ji cewa Rundunar 'yan sandan jihar Kaduna ta kama wasu mutane 165 da kuma ababen hawa 205 sakamakon karya dokar ta-bacin da aka saka a jihar don hana yaduwar cutar COVID-19.

Wannan na kunshe ne a takardar da kakakin rundunar 'yan sandan jihar, ASP Mohammed Jalige ya fitar a ranar Litinin.

Ya yi kira ga jama'a da su kasance masu bin doka, kiyaye dokokin hana yaduwar cutar da kuma ci gaba da zama a gida don tabbatar da lafiyar jama'ar jihar, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel