Hamshakin mai kudi yayi alkawarin ciyar da mutane 100,000 a jihar Legas a wannan lokaci na Coronavirus

Hamshakin mai kudi yayi alkawarin ciyar da mutane 100,000 a jihar Legas a wannan lokaci na Coronavirus

- Sanannen dan kasuwa wanda ya kware a kasuwancin kadarori ya bayyana cewa zai tallafawa jama'ar jihar Legas

- Ya bayyana cewa gidauniyar shi za ta ciyar da a kalla jama'a 100,000 da kayan abinci da sauran kayayyakin bukata

- Dan kasuwar ya yi kira ga jama'a da ke jihar Legas da su kira gidauniyar don bayyana musu wuraren da ake bukatar tallafin

Olu Okeowu sanannen dan kasuwa dan kasuwa ne kuma mai taimakon jama'a. Ya shirya tsaf don taimakon 'yan kasar nan da ke fama da dokokin hana yaduwar muguwar cutar coronavirus. Yana taimakon jama'a ne don taimakawa kokarin gwamnati wajen ragewa jama'a matsalar kullen da suke ciki a kan cutar coronavirus.

Hamshakin mai kudi yayi alkawarin ciyar da mutane 100,000 a jihar Legas a wannan lokaci na Coronavirus

Hamshakin mai kudi yayi alkawarin ciyar da mutane 100,000 a jihar Legas a wannan lokaci na Coronavirus
Source: Facebook

A kokarinsa na taimakon al'ummar da suka daga sunansa, Okeowu, ta karkashin gidauniyarsa ya kaddamar da shirin samar da abinci ga mutane 100,000 da sauran ababen bukata. Burinshi ya hada da fatattakar yunwa a jihar Legas.

KU KARANTA: Ka dakatar da karbar kudin wuta da ruwa na tsawon wata biyu - Dan majalisar wakilai Shehu Koko ya roki shugaba Buhari

Wajen raba kayan abincin kamar yadda ya bayyana suna nan a tsibiri da kuma cikin garin Legas din kamar yadda shafin Linda Ikeji ya bayyana.

Gidauniyar ta kara da kira ga mazauna jihar da su nemi taimakonta matukar bukatar hakan ta taso. Su kuma bayyana duk inda suka san akwai mabukata don gidauniyar ta tallafa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Online view pixel