Madalla: Hadiza Isma El-Rufai ba ta dauke da kwayar cutar COVID-19

Madalla: Hadiza Isma El-Rufai ba ta dauke da kwayar cutar COVID-19

A jiya ne ku ka ji cewa Uwargidar jihar Kaduna, Hadiza Isma El-Rufai ta yi gwajin kwayar cutar COVID-19 domin tabbatar da halin da lafiyarta ta ke ciki.

A halin yanzu mun ji labari cewa sakamakon wannan gwaji da Hajiya Hadiza Isma El-Rufai ta yi a Ranar Lahadi ya fito, kuma ba ta kamu da wannan cuta ba.

Hadiza Isma El-Rufai ta bayyanawa Duniya wannan ne a shafinta na Tuwita kamar yadda ta saba tattaunawa da dinbin Mabiyanta da su ka haura mutum 50, 000.

A Jiya Isma El-Rufai ta rubuta: “Ya ku mutanen dandalin Tuwita, sakamakon gwajin kwayar cutar COVID-19 da na yi ya fito. Ba na dauke da cutar a jiki na.”

Uwargidar mai girma Nasir El-Rufai ta jihar Kaduna ta kara da cewa: “Na gode da duka addu’o’i da fatan alherinku” A karshe kuma ta godewa Allah Madaukaki.

KU KARANTA: Gwaji ya nuna wani Gwamnan Najeriya ya na dauke da COVID-19

Matar gwamnan ta yi kira ga jama’a su rika wanke hannunsu, sannan kuma su rika zama a cikin gida kamar yadda hukumomi da gwamnati su ka bada umarni.

Wadannan hanyoyi duk su na cikin sharudan da aka gindaya domin kare lafiyar jama’a. Ana kyautata zaton rage yaduwar cutar idan mutane su ka zauna a gida.

Jama’a sun fito sun nuna farin cikinsu bayan samun labarin cewa Hadiza Isma El-Rufai ba ta kamu da wannan cuta da Mai gidanta Nasir El-Rufai ya kamu da ita ba.

Hakan na nufin yawan masu dauke da cutar COVID-19 ya tsaya a mutane biyu a Kaduna. NCDC ta bayyana cewa kawo yanzu mutane 131 ke dauke da cutar a Najeriya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Online view pixel