Annobar coronavirus: An gurfanar da wani limami da wadanda ya jagoranta sallah a Kaduna

Annobar coronavirus: An gurfanar da wani limami da wadanda ya jagoranta sallah a Kaduna

A ranar Litinin ne wata kotun Majistare da ke zamanta a kan titin Ibrahim Taiwo da ke garin Kaduna ta bayyana cewa Muhammad Umar, malamin addinin Musulunci da ya take dokar jihar Kaduna na hana jam'i, zai biya naira miliyan daya a matsayin kudin beli.

Umar, tare da Yusuf Hamza, Muhammad Ubale, da Auwal Shuaibu, duk mazauna Unguwan Kanawa da ke Kaduna, an kama su da laifin hadin kai wajen karantsaye ga dokar jiha.

Alkali Ibrahim Musa, ya bayyana cewa Hamza, Ubale da Shuaibu duk za a yi belinsu a kan naira miliyan dai-dai.

Alkalin ya bawa masu kare kansu umarnin samar da mutum biyu da zasu tsaya musu, wadanda dole su zama mazauna cikin Kaduna.

"Na bada umarnin a tsareku a wajen 'yan sanda a maimakon gidan gyaran hali saboda cutar Coronavirus har zuwa lokacin da zaku cika sharuddan belinku." Alkalin yace.

"Wadanda zasu tsaya muku dole su zama ma'aikatan gwamnati da ke matakin aiki a kalla na 14 kuma su zama sun mallaki shaida tare da asusun banki wanda a kalla za a samu naira miliyan daya." a cewarsa.

Annobar coronavirus: An gurfanar da wani limami da wadanda ya jagoranta sallah a Kaduna

An gurfanar da wani limami da wadanda ya jagoranta sallah a Kaduna
Source: Twitter

Tun farko dai, daraktan gurfanarwa na jihar Kaduna, Bayero Dari, ya ce laifinsu ya ci karo da tanadin sashi na 59 da na 115 na dokokin laifukan jihar Kaduna.

Ya ce a ranar 29 ga watan Maris, wajen karfe 4:30 na yamma ne aka mayar da binciken mutanen karkashin rundunar 'yan sanda ta musamman mai binciken manyan laifuka na jihar Kaduna wacce ke ofishin 'yan sanda na Kawo, Kaduna.

DUBA WANNAN: Jagorantar Sallar Juma'a: Sheikh Jingir ya saduda bayan ya amsa gayyatar DSS

"A ranar 27 na watan Maris ne bayani yazo da ke bayyana cewa babban limamin Unguwan Kanawa, Malam Muhammad Umar, ya jagoranci sauran mutane uku da ke kare kansu tare da wasu mutane 17 don sallar Azahar," a cewarsa.

Sai dai, ya roki kotun da ta dage sauraron shari'ar don ya samu damar gabatar da shaidu.

A bukatar lauyan wadanda ake kara, Abdulbasit Sulaiman, ya bukaci kotun da ta bada belin wadanda yake karewa.

"Ina rokon kotun nan da ta bada belin wadanda nake karewa karkashin sashin na 35 da 36 na kundin tsarin mulkin shekarar 1999.

"Mun yi alkawarin zasu zama masu dabi'a ta gari kuma ba za su shiga abinda zai hana bincike. Zai zama babbar illa gareu idan aka mika su gidan gyaran hali", Sulaiman yace.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel