Sakon faifan bidiyo zuwa ga Buhari: Janar a rundunar ya fadi gaskiyar halin da suke ciki a Borno

Sakon faifan bidiyo zuwa ga Buhari: Janar a rundunar ya fadi gaskiyar halin da suke ciki a Borno

Wani soja mai mukamin manjo janar a rundunar sojin Najeriya mai suna Olusegun Adeniya ya bayyana cewa hare-haren mayakan Boko Haram a garesu na ci gaba da tsananta a kwanakin nan da suka shude.

A wani bidiyo da ya fara yawo a yanar gizo, Adeniyi, wanda ke filin fama a jihar Borno, an ji yana bayyana cewa 'yan ta'addan sun mallaki makaman zamani kuma suna kare duk wani martani da suka mayar musu da salo na musamman.

Ya ce: "Muna fuskantar matsananciyar tirjiya daga mayakan Boko Haram. Suna da makaman zamani fiye da na rundunar soji. Da safiyar yau, a kalla motocin yaki 15 ne suka fuskancemu. Sun harbo mana rokoki sama da dari," Olusegun Adeniyi, manjo janar kuma kwamandan rundunar Operation Lafiya Dole, ya sanar a bidiyon.

A wannan bidiyon, Adeniyi ya ce shi da sauran masu mukamin janar a rundunar sojin ne suka jagoranci dakarun don fuskantar 'yan ta'addan.

"Duk da haka, bamu tsere mun barsu ba. Ni da sauran masu mukamin Janar din ne muka jagoranci fadan. Muna fuskantarsu amma gaskiyar abinda ke faruwa kenan," ya kara da cewa.

A yayin daukan faifan bidiyon, an haska wasu dakarun soji da ke kwance cikin jini bayan musayar wuta da mayakan kungiyar Boko Haram.

DUBA WANNAN: An tabbatar da samun kwayar cutar coronavirus a jikin sojoji biyu a Maiduguri

Janar Adebiyi ya bayyana cewa babu wani Janar din soji da ya gudu ko kuma yake kin jagorantar bataliyar sojoji domin yakar 'yan Boko Haram, amma maganar gaskiya ita ce, "mayakan kungiyar Boko Haram suna da shiri sosai, suna da manyan makamai na zamani da babu irinsu a hannun dakarun sojoji."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel