Annobar coronavirus: Gwamnatin tarayya ta shigar da karar wasu manyan shaguna 4 saboda kara farashin kaya

Annobar coronavirus: Gwamnatin tarayya ta shigar da karar wasu manyan shaguna 4 saboda kara farashin kaya

Hukumar kula, bayar da kariya da kare hakkin masu siyayya (FCCPC) ta shigar da karar wasu manyan shagunan sayar da kayan amfani da magunguna guda hudu da ke birnin tarayya, Abuja.

Za a gurfanar da manyan shaguna gudu hudu ne bisa zarginsu da kara farashin kayan tsaftace muhalli, sinadarin tsaftace hannu, da sauran kayan amfani da jama'a ke bukata a wannan lokaci da ake fama da annobar cutar coronavirus.

A takardar karar da jaridar Premium Times ta yi ikirarin cewa ta gani, manyan shagunan sune; babban shagon sayar da kaya mai suna Prince Ebeano da mai shagon, David Ojei, da shagon sayar da magunguna mai suna 'Bakan Gizo' da wakilan shagon, Ray Opia da Luta Irene.

Annobar coronavirus: Gwamnatin tarayya ta shigar da karar wasu manyan shaguna 4 saboda kara farashin kaya
Babban shagon sayayya
Asali: Getty Images

Sauran manyan shagunan sune; babban shagon sayar da magunguna da kayan amfani mai suna 'H-Medix' da wakilansu, Sandra Ejekwu da John Oluwagbemiga, da kuma shagon 'Faxx Stores & Trading Limited' da wakilinsu, Adogah Ahmed.

DUBA WANNAN: Jagorantar Sallar Juma'a: Sheikh Jingir ya saduda bayan ya amsa gayyatar DSS

Hukumar FCCPC ta shirya tuhuma guda shidda a cikin takardar karar da ta shigar a gaban wata babbar kotun tarraya da ke Abuja.

Daga cikin laifukan da ake zarginsu da aikatawa akwai karya, yaudara, hada baki, da amfani da annobar cutar coronavirus don tsawwalawa jama'a da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng