Covid-19: Sakamakon gwaji ya nuna mutane 5 da ake zargin sun kamu a Borno basa dauke da cutar

Covid-19: Sakamakon gwaji ya nuna mutane 5 da ake zargin sun kamu a Borno basa dauke da cutar

- Kwamishinan lafiya na jahar Borno, Dr. Salisu Kwayabura ya bayyana cewar sakamakon gwajin coronavirus da aka yiwa wasu mutane biyar da ake zargin sun kamu a jahar ya fito

- Kwayabura ya tabbatar da cewar dukkaninsu babu mai dauke da cuar ta covid-19

- Ya kuma jadadda cewar cibiyar lafiya da ayyukan gaggawa na aiki a matakan da ya dace sannan kuma a shirye suke tsaf domin magance kowani lamarin gaggawa a jahar

Kwamishinan lafiya na jahar Borno, Dr. Salisu Kwayabura, ya tabbatar da cewar dukkanin mutane biyar da ake zargin suna dauke da cutar coronavirus a jahar basa dauke da cutar.

Kwayabura wanda ya yi jawabi ga manema labarai a yammacin ranar Lahadi, 29 ga watan Maris a Maiduguri ya ce an kebe mutanen ne a cibiyar kiwaon lafiya na jahar, inda ya bayyana cewa “mutanen biyar su da kansu suka gabatar da kasu domin yi masu gwaji biyo bayan tafiya da suka yi zuwa kasashen da ke fama da annobar ta coronavirus sosai.”

Covid-19: Sakamakon gwaji ya nuna mutane 5 da ake zargin sun kamu a Borno basa dauke da cutar

Covid-19: Sakamakon gwaji ya nuna mutane 5 da ake zargin sun kamu a Borno basa dauke da cutar
Source: Depositphotos

Ya yi bayanin cewa: “Sakamakon gwaji daga samfurin da aka dauka na mutanen su biyar domin yin gwaji a cibiyar hana yaduwar cututtuka na Abuja, ya dawo kuma ya nuna basa dauke da cutar ta covid-19.”

A cewarsa: “Cibiyar lafiya da ayyukan gaggawa na aiki a matakan da ya dace sannan kuma a shirye suke tsaf domin magance kowani lamarin gaggawa a jahar.”

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Ku cika gidajenku da kayan abinci – Minista ga mata

A wani labarin kuma mun ji cewa Gwamnan jahar Kwara, Abdulrahman Abdulrazak ya bayyana cewa ya sadaukar da albashinsa na watanni 10 domin ganin an dakatar da yaduwar annobar Coronavirus a Najeriya.

Premium Times ta ruwaito gwamnan ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da ya fitar da yammacin Lahadi, 29 ga watan Maris, a daidai lokacin da attajiran Najeriya suke bayar da nasu gudunmuwar domin taimaka ma gwamnati wajen yaki da cutar.

A cikin wannan sanarwa da Gwamna Abdulrahman Abdulrazak ya fitar ya bayyana cewa tun daga lokacin da ya zama gwamnan jahar Kwara ba’a taba biyansa albashi ba, don haka yana bukatar albashin a yanzu domin a kashe su wajen yaki da Corona, duk da cewa ba’a samu bullarta a jaharsa ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel