Jagorantar Sallar Juma'a: Sheikh Jingir ya saduda bayan ya amsa gayyatar DSS
Shugaban kungiyar Jama'atu Izalatil Bid'ah Wa Ikamatis Sunnah, JIBWIS, Sheikh Yahaya Jingir ya bayyana biyayyarsa ga gwamnatin jihar Filato, bayan tambayoyin da ya amsa daga wajen hukumar jami'an tsaro ta fararen kaya a kan zarginsa da take dokar hana walwala a jihar don hana yaduwar muguwar cutar Coronavirus.
Idan zamu tuna, Jingir ya jagoranci jama'a masu tarin yawa don sallar Juma'a a masallacin Yantaya a ranar Juma'a da ta gabata, duk kuwa da umarnin gwamnatin jihar na hana taron da ya kai mutane 50.
Wata majiya mai karfi wacce ke da kusanci da Gwamna Simon Lalong ta tabbatar da cewa jami'an hukumar 'yan sandan farin kaya sun gayyaci Sheikh Jingir.
"An gayyaci babban malamin addinin don amsa wasu tambayoyi," majiyar ta sanar da wakilin jaridar Daily Nigerian.
Wata majiya ta kusa da hedkwatar jami'an tsaron fararen kayan ta kara tabbatar da cewa an tuhumi malamin. A cewar majiyar: "Manyan jami'ai daga babban ofishinmu na Abuja sun zo kuma sun gayyaci Sheikh Jingir a ranar Asabar da kuma Lahadi. An tuhume shi amma daga baya sai aka barshi ya tafi gida,"
A lokacin da aka tuntubi sakataren yada labarai na JIBWIS din, Ahmad Ashir ya ce bai san cewa an tuhumi shugaban nasu ba.
A wannan halin, kwamitin zartarwa na JIBWIS ta fitar da takarda a daren Lahadi wacce ke nuna cewa sun yi biyayya ga duk umarnin kiwon lafiya da na hana yaduwar cutar da gwamnatin tarayya da na jihohi suka bada don hana yaduwar COVID-19 a Najeriya.
Shugaban gudanarwa na JIBWIS din na kasa, Sheikh Nasiru AbdulMuhyi, wanda yasa hannu a takardar, ya jaddada goyon bayansu ga dabarun gwamnatin na hana yaduwar muguwar cutar.
DUBA WANNAN: Saudiyya ta sanar da warkewar mutum 66 da suka kamu da kwayar cutar COVID-19 (bidiyo)
Kamar yadda kungiyar ta bayyana, duk wani mataki na gwamnati don kariya ga lafiya da kuma jin dadin 'yan Najeriya, abin runguma ne a wannan lokaci na tsanani.
Kungiyar ta kara da bayyana dakatar da gasar mahaddata Qur'ani ta kasa da za ta yi.
Ta tabbatar wa hukumomi na kowanne matakin gwamnati a kan cewa ta kammala shirye-shiryen wayar da kai a kan nesanta, taro, killace kai da sauran matakan tsafta da yakamata jama'a su kiyaye don gudun yaduwar muguwar cutar covid-19.
"Muna jajantawa wadanda suka kamu da cutar tare da yi musu addu'a samun waraka daga Allah," takardar tace.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng