Coronavirus: Ba mutanen da ya kamata ayi wa gwaji muke yiwa ba – Gwamnan Niger

Coronavirus: Ba mutanen da ya kamata ayi wa gwaji muke yiwa ba – Gwamnan Niger

- Gwamna Abubakar Sani Bello na jahar Niger ya soki tsarin gwajin da hukumar NCDC ke amfani dashi

- Gwamnan jahar Niger ya ce mayar da hankali da aka yi kan rukunin wasu mutane da ke da coronavirus ba daidai bane

- Bello ya ce ba daidai bane a dunga dauke idanu daga kan marasa galihu a lamarin Covid-19 yayinda aka mayar da hankali kacokan a kan manyan mutane

Gwamnan jahar Niger, Alhaji Abubakar Sani Bello, ya caccaki tsarin da hukumar NCDC ke amfani dashi wajen zabar wadanda za a yiwa gwajin cutar coronavirus.

Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Gwamna Bello ya bayyana a ranar Lahadi, 29 ga watan Maris, cewa mayar da hankali da aka yi kan rukunin wasu mutane da coronavirus ya kama ba daidai bane.

Ya ce kokarin Najeriya wajen hana yaduwar cutar ba lallai bane ya haifar da yaya masu idanu idan har aka ci gaba da dauke idanu a kan mutane marasa galihu kan lamarin Covid-19 yayinda aka mayar da hankali a kan manyan mutane.

Coronavirus: Ba mutanen da ya kamata ayi wa gwaji muke yiwa ba – Gwamnan Niger
Coronavirus: Ba mutanen da ya kamata ayi wa gwaji muke yiwa ba – Gwamnan Niger
Asali: UGC

“Muna dauke idanu a kan marasa galihu sannan muna mayar da hankali ga manyan yan siyasa, yan kasuwa ko shugabannin addinai,” in ji gwamnan.

Hukumar NCDC ta mayar da kai ga rukunin mutane biyu da take yiwa gwajin Covid-19. Wadannan mutane sune wadanda ke da tarihi na fita wajen Najeriya da ke da zazzabi, tari ko wahalar numfashi cikin kwanaki 14 da dawowarsu da kuma wadanda suka hadu da wadanda aka tabbatar suna da cutar .

KU KARANTA KUMA: Na bada kyautar albashina na wata 10 domin yaki da Coronavirus – Gwamnan Kwara

A wani labari na daban, mun ji cewa yan majalisar dokokin jahar Kaduna sun shiga alhini da rudani sakamakon sanarwar da Gwamna Malam Nasir El-Rufai ya yi a ranar Asabar, na cewar sakamakon gwaji ya nuna yana dauke da cutar Coronavirus.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa sanarwar da El-Rufai ya yi ya sanya fargaba a zukatan wasu yan majalisa musamman wadanda suka yi aiki dab da dab dashi a makon da ya gabata, domin basu na san ya yi gwajin ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel