Dakarun Sojin Najeriya sun aika yan bindiga 9 barzahu, sun ceto mutane 12 a Zamfara

Dakarun Sojin Najeriya sun aika yan bindiga 9 barzahu, sun ceto mutane 12 a Zamfara

Dakarun rundunar Sojin Najeriya dake aikin Operation Hadarin Daji sun ceto mutane 12 daga hannun masu garkuwa da mutane a karamar hukumar Bungudu ta jahar Zamfara, daga cikinsu har da hakimin Wuya.

Gidan talabijin na Channels ta ruwaito mukaddashin daraktan watsa labaru na hukumar Sojin Najeriya, Birgediya Janar Benard Onyeuko ne ya bayyana haka a ranar Lahadi, 29 ga watan Maris, inda yace Sojojin sun kama yan bindiga 9, sun kama 14 a Zamfara.

KU KARANTA: Annobar Corona: Al’ummar jahar Kano sun tashi da azumi domin neman taimakon Allah

Birgediya Onyeuko ya bayyana cewa Sojoji sun banka wuta a gidaje 13 mallakin gungun yan bindiga daban daban a garuruwan Gidan Usman, Gidan Babagoji, Gadauna, Gidan Janari, Kekuwa, Gidan Sarki, Gardi da Binhgi.

“Dakarun Operation Hadarin Daji a jahar Zamfara sun halaka yan bindiga da dama a makon da ta gabata, tare da kubutar da mutane 12 da aka yi garkuwa da su, daga cikinsu har da hakimin Wuya, wanda aka yi garkuwa da shi a makon da ta gabata.

“Haka zalika a yayin samamen da Sojoji suka kai a garuruwan Gidan Usman, Gidan Babagoji, Gadauna, Gidan Janari, Kekuwa, Gidan Sarki, Gardi da Bingi, duk a cikin karamar hukumar Bungudu na jahar Zamfara, sun kashe yan bindiga 9, sun kama 14, kuma sun kona gidaje 13. Bugu da kari Sojoji sun kwato shanu 67, kuma tuni suka mikasu ga hakiman yankin.” Inji shi.

A wani labari kuma, Sojoji sun kama wasu yan bindiga guda 9 yayin da suke sintiri a kauyen Nasarawa dake karamar hukumar Gusau ta jahar Zamfara, inda suka kama akalla shanu 600 da tumaki 300.

Sai dai yayin da suke amsa tambayoyi, yan bindigan sun bayyana cewa sun sato dabbobin ne a Zamfara, kuma suna hanyar kai su garin Zaria ta jahar Kaduna domin sayar dasu, tare da kauce ma shiga hannun hukuma.

Daga karshe Birgediya Onyeuko ya bayyana cewa a yanzu dabbobi 900 suna hannun Sojojin Operation Hadarin Daji, kuma za su mikasu ga masu su da zarar sun tabbatar da mamalakkansu.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel