Tinubu ya fitar da Naira Miliyan 200 na maganin COVID-19 a Najeriya

Tinubu ya fitar da Naira Miliyan 200 na maganin COVID-19 a Najeriya

Jigon jam’iyyar APC mai mulki, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu, ya bada sanarwar cewa ya bada gudumuwar makudan miliyoyin kudi da nufin a yaki Coronavirus.

Alhaji Bola Ahmed Tinubu ya bada kyautar Naira miliyan 200 domin kawo hanyoyin yakar annobar cutar COVID-19 da yanzu ta ratsa kashe fiye da 190 a Duniya.

Tsohon gwamnan wanda ya cika shekaru 68 a karshen makon da ya gabata ya bayyana wannan ne a wani jawabi da ya fitar da hannunsa bayan fasa bikin mauludinsa.

A duk shekara irin wannan lokaci, Tinubu ya kan shirya gagarumin biki domin a taya sa murnar zagayowar ranar haihuwarsa, a bana annobar COVID-19 ta hana taron.

Bola Tinubu wanda ya cika shekarau 68 ya yabawa mutanen jihar Legas da su ka bi matakan da aka gindaya na rage cakuduwar jama’a domin rage yaduwar Coronavirus.

KU KARANTA: Mataimakin COS Abba Kyari ya kamu da COVID-19 - Rahotanni

Tinubu ya fitar da Naira Miliyan 200 na maganin COVID-19 a Najeriya

Tsohon Gwamnan Legas Tinubu zai bada Miliyoyi na yaki da COVID-19
Source: Depositphotos

‘Dan siyasar ya fasa yin wannan taro ne domin bin ka’idar da gwamnati ta sa na rage cunkuso. Duk da cewa ba a iya yin taron ba, Tinubu ya yi abin da za a dade ana yabawa.

“Yayin da na ke nadamar halin da ya sa mu ka gaza taruwa domin murnar zagayowar ranar haihuwata, duk da haka zan bada kudi domin tunawa da wannan rana.”

“A dalilin haka na zabi in sanar da cewa zan bada kyautar Naira miliyan 200 domin yaki da wannan muguwar cuta. Zan bada Naira miliyan 100 ga gwamnatin Legas.”

Ya ce: "Da kuma wata Naira miliyan 100 domin taimakawa hukumar takaita cuta ta Najeriya watau NCDC wajen kokarin da ta ke yi na ganin bayan annobar COVID-19.”

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel