COVID-19 ta kashe tsohon ‘Dan wasa Mohammed Farah - SFF
Kasar Somaliya ta yi rashin tsohon ‘Dan kwallonta, Abdulkadir Mohamed Farah. Tsohon ‘Dan wasan ya mutu ne a sakamakon jinya da ya yi na cutar Coronavirus.
Hukumar kwallon kafan kasar Somalia, ta tabbatar da rasuwar Abdulkadir Mohamed Farah a Ranar 27 ga Watan Maris, 2020, kamar dai yadda mu ka samu labari.
Marigayi Abdulkadir Mohamed Farah ya rasu ne tun a Ranar Talata watau 24 ga Watan Maris, a wani asibiti mai suna Northwest London Hospital da ke kasar Ingila.
Shugaban hukumar kwallon kafan Somaliya, Abdiqani Said Arab, ya bada wannan sanarwa. Kafin Mohamed Farah ya cika, an gano ya na dauke da cutar COVID-19.
Abdiqani Said Arab ya aikawa ‘Yanuwan Marigayin ta’aziyya a madadin hukumar da kuma gwamnatin Somaliya da daukacin al’ummar wannan kasa ta Afrika.
KU KARANTA: Malaman asibiti sun kamu da COVID-19 a Jami’ar Najeriya
Said Arab ya ce kafin rasuwar Abdulkadir Mohammed Farah ya na cikin masu bada shawara ga babban Ministan harkokin matasa da wasannin kasar Somaliya.
Tarihi ya nuna cewa an haifi Marigayi Mohamed Farah ne a wani Gari mai suna Beledweyne da ke kimanin kilomita 300 da babban birnin kasar watau Mogadishu.
Tsohon ‘Dan wasan ya bar Duniya ya na da shekaru kusan 69. Farah ya fara taka leda ne a shekarar 1976 a matsayin ‘Dan kwallo a gasar Makarantun kasar Somaliya.
Daga nan ne tauraruwar Mohamed Farah ta rika haskawa har ta kai an san shi a Somaliya. Farah ya cigaba da buga kwallo har zuwa karshen shekarun 1980s a Duniya.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng