A karshe: Buhari zai gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan kasa da yamma

A karshe: Buhari zai gabatar da jawabi kai tsaye ga 'yan kasa da yamma

Da yammacin yau, Lahadi, ne shugaban kasa, Muhammadu Buhari, zai gabatar da jwabi kai tsaye ga 'yan Najeriya, kamar yadda wata sanarwa daga fadar shugaban kasa ta bayyana.

A wani sako da Bashir Ahmad, mataimaki na musamman ga shugaba Buhari, ya fitar a shafinsa na tuwita, ya bayyana cewa shugaban kasar zai gabatar da jawabin ne da misalin karfe 7:00 na yamma.

Ya bayyana cewa za a iya sauraro ko kallon jawabin na shugaba Buhari a gidajen radiyo da talabijin da ke fadin kasar nan, musamman gidajen talabijin da radiyo mallakar gwamnatin tarayya.

A ranar 22 ga watan ne Obinna Simon, wani dan Najeriya mai wasan barkwanci da ke matukar kama da shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya saki wani jawabi ga 'yan kasa inda a cikinsa ya yi magana a kan bullar annobar kwayar cutar coronavirus.

Fitaccen mai wasan barkwancin, wanda aka fi sani da 'MC Tagwaye', ya saki jawabin ne a daidai lokacin da 'yan Najeriya ke cigaba da guna-guni a kan jinkirin da shugaba Buhari ke yi wajen gabatar da jawabi ga 'yan kasa a kan annobar coronavirus.

Kamar yadda ya saba yin magana cikin kwaikwayon muryar Buhari, MC Tagwaye ya bukaci 'yan Najeriya su mayar da hankali wajen biyayya ga hanyoyin dakile yaduwar COVID-19.

DUBA WANNAN: Mugun ciwo ne, ina jin jiki; ku tayani da addu'a - Matar da ta kamu da coronavirus

A ranar 23 ga wata, Legit.ng ta wallafa rahoton cewa bayan dogon lokacin da shugaban kasan Najeriya, Muhammadu Buhari, ya dauka bai ce komai a kan muguwar cutar Covid-19 ba, daga baya ya yi magana tare da jawabi a kan matakan da gwamnatinsa ke dauka a kan yaduwar kwayar cutar.

A dan gajeren bidiyon da shugaban yayi jawabi a kan cutar, ya ce "Muna aiki tare da ma'aikatar lafiya domin ganin mun kare 'yan kasarmu daga annobar coronavirus."

Ya kara da cewa, "A matsayinmu na gwamnati, wannan ne abin da muka fi mayar da hankali a kai. Sakamakon hakan ne muke kira gareku a kan tabbatar cewa ku kiyaye dukkan hanyoyin kariya daga kamuwa da cutar."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng