Rundunar 'yan sanda ta ankarar da jama'a a kan sabon salon damfara da sunan COVID-19

Rundunar 'yan sanda ta ankarar da jama'a a kan sabon salon damfara da sunan COVID-19

Babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya (IGP), Mohammed Adamu, ya bukaci jama'ar Najeriya a kan su kara lura tare da daukan matakan kare kansu daga sharrin mugwayen mutane da ke amfani da bullowar annobar covid-19 domin damfarar mutane.

IGP ya bayar da wannan shawara ne bayan sashen binciken sirri na rundunar 'yan sanda ya mika masa rahoton da ke nuna cewa masu laifi, musamman damfara ta hanyar yanar gizo, zasu yi amfani da dokar hana mutane fita da rufe wuraren aiki da kasuwanci domin fadada mugun aikinsu.

Hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, DCP Frank Mba, ya fitar a Abuja ranar Lahadi.

A cewar jawabin, ruundunar 'yan sanda ta samu bayanan da ke nuna cewa wasu 'yan damfara sun fara amfani da dandalin sada zumunta da sauran kafofin aike sako ta yanar gizo domin neman jama'a su cike bayanansu domin kawo musu maganin kwayar cutar covid-19 har inda suke.

Rundunar 'yan sanda ta ankarar da jama'a a kan sabon salon damfara da sunan COVID-19

IGP Adamu Abubakar
Source: UGC

"A wasu lokutan, masu damfarar kan yi amfani da sunan fitattun kamfanonin sarrafa magunguna da sayar da su don mutum ya saki jiki da su, sannan daga baya sai su nemi ya aika musu kudin magungunan daga asusunsa," a cewar jawabin.

DUBA WANNAN: Jerin jihohin Najeriya 12 da aka tabbatar da bullar kwayar cutar coronavirus

Jawabin ya kara da cewa, rundunar 'yan sanda na shawartar jama'a su lura sosai kafin bude sakonnin da aka aiko musu ta kafafen aike sako na yanar gizo tare da kula da duk wani shafi da zasu ziyarta a yanar gizo.

Kazalika, jawabin ya yi kira ga jama'a da su gaggauta kai rahoton duk wata lambar waya da aka kirasu da ita tare da neman su aika kudi domin biyan kudin maganin wani dan uwansu da aka killace a cibiyar tattara masu dauke da kwayar cutar coronavirus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel