Otegbayo, Olapade-Olaopa da Denloye su na dauke da kwayar COVID-19
Labari ya zo mana cewa shugaban asibitin da ke jami’ar Ibadan, Farfesa Jesse A Otegbayo ya tabbatar da cewa ya kamu da cutar Coronavirus a halin yanzu.
Jesse A Otegbayo ya bada wannan sanarwa ne a wani jawabi da ya fitar da hannunsa. Jesse A Otegbayo ya kamu da wannan cuta ne a taron da su ka yi kwanaki.
Farfesa Otegbayo ya ce bayan sun fara gudanar da wani taro na shugabannin asibitin UCH a makon jiya, sai su ka fahimci Abokin aikinsu ya kamu da COVID-19.
Otegbayo ya shaidawa ‘Yan jarida cewa wannan ya sa su ka dakatar da taron, sannan kuma aka yi wa wannan Bawan Allah gwaji, inda aka tabbatar ya kamu da cutar.
A dalilin haka, Jesse A Otegbayo da sauran Likitoci su ka killace kansu, sannan aka yi masu gwaji. Bayan sakamako ya fita, an gane cewa cutar ta kama Likitan
KU KARANTA: An samu labarin sakamakon gwajin COVID19 da Sanusi II ya yi a Legas
Yanzu haka dai shugaban asibitin ya kebe kansa, ya kuma yi kira ga jama’a su guji yawace-yawacen da zai iya jefa jama’a cikin hadarin kamuwa da Coronavirus.
A daidai wannan lokaci kuma wani labari maras dadi irin wannan ya fito daga Jaridar Vanguard, inda aka ji cewa wasu manyan Likitoci biyu sun kamu da wannan cuta.
Shugaban tsangayar sashen kiwon lafiya a jami’ar ta Ibadan da Mataimakinsa watau Farfesa Ezekiel Olapade-Olaopa da kuma Farfesa Obafunke Denloye duk sun kamu.
Farfesa Olapade-Olaopa ya bayyanawa ‘Yan jarida ta sakon WhatsApp cewa gwajin da su ka yi ya nuna cewa shi da Mataimakin na sa su na dauke da kwayar Coronavirus.
Ko da alamomin cutar ta COVID-19 ba ta fara bayyana baro-baro a jikin wadannan manyan Likitoci ba, sun bayyana cewa duk da haka sun killace kansu daga jama’a.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng