A dakatar da VAT, a rage haraji da ruwan da ke cikin bashin banki – Tinubu ga Buhari

A dakatar da VAT, a rage haraji da ruwan da ke cikin bashin banki – Tinubu ga Buhari

A daidai lokacin da Duniya ta ke fama da annobar Coronavirus, jagoran jam’iyyar APC, Bola Ahmed Tinubu ya bada shawararin matakan da ya kamata gwamnatin Najeriya ta dauka.

Asiwaju Bola Tinubu ya bayyana cewa Najeriya ba za ta iya cin karfin Coronavirus idan har cutar ta barke kamar yadda ake fama da lamarin a kasashen Turai da kuma Nahiyar Amurka ba.

Bola Tinubu ya yi wannan magana ne a jawabin da ya yi bayan ya cika shekaru 68 a Ranar Juma'a. Tinubu ya kuma yi kira ga mutane su bi sharudan da hukumomi su ka gindaya.

A jawabin na sa, Bola Tinubu ya yi kira ga gwamnatin tarayya da ta kara adadin kudin da kasar ta ke bugawa a halin yanzu domin a samu a ga bayan wannan muguwar cuta ta COVID-19.

A cewar ‘Dan siysar, farashin gangar mai ya karye, wanda hakan zai jawowa Najeriya karancin Dala. A ganinsa, wannan bai nuna dole sai an samu karancin kudin kashewa na gida.

KU KARANTA: Masu dauke da cutar COVID-19 sun doshi mutum 100 a Najeriya

A dakatar da VAT, a rage haraji da ruwan da ke kan bashin banki – Tinubu ga Buhari
Tinubu ya ce lokacin da ake fama da annobar COVID-19, ba lokacin siyasa ba ne
Asali: Facebook

Bayan haka, Bola Tinubu ya bukaci gwamnatin shugaban kasa Muhammadu Buhari ta dakatar da karbar karin kudin harajin VAT. Kwanaki aka maida harajin VAT ya koma 7.5% a Najeriya.

Haka zalika, ba tare da wani bata lokaci ba, Tinubu ya nemi babban bankin Najeriya na CBN ya rage ruwan da ke kan bashi. Tinubu ya kuma nemi a rage harajin da aka laftawa kamfanoni.

Jagoran na jam’iyya mai mulki ya bayyana cewa dakatar da karbar VAT na watanni biyu ko hudu zai taimakawa tattalin arzikin Najeriya wajen ganin farashin kaya ba su tashi a kasuwa ba.

Jawabin tsohon gwamnan ya nuna cewa dole gwamnati ta yi da gaske wajen ganin abinci bai yi wahala ba. Tinubu ya bada shawarar a dauki matakin hana kayan amfanin gona lalacewa.

Tinubu ya kuma roki IMF da Bankin Duniya su dakatar da karbar biyan bashinsu. A karshe, Jigon na APC ya yi kira ga jama’a su ajiye duk wani banbancin akida ko siyasa, su hada-kai.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel