COVID-19: 'Yan Najeriya sun bukaci a damke Sheikh Jingir bayan ya ja sallar Juma'a (Bidiyo)

COVID-19: 'Yan Najeriya sun bukaci a damke Sheikh Jingir bayan ya ja sallar Juma'a (Bidiyo)

- 'Yan Najeriya da yawa ne suka bukaci gwamnati da ta damke Sheikh Sani Yahaya Jingir, shugaban Musulmi mabiya akidar Izala

- Tuni dama dai babban malamin ya kwatanta cutar coronavirus farfagandar turawan yamma tare da karyata wanzuwar cutar

- A yau dai Juma'a ne ya ja sallar Juma'a a garin Jos na jihar Filato duk da kuwa gwamnatin jihar ta haramta duk wani taron jama'a da zai kai mutane 50

'Yan Najeriya masu tarin yawa sun garzaya kafar sada zumuntar zamani inda suke bukatar a damke shugaban Izala bayan da ya jagoranci sallar Juma'a a ranar 26 ga watan Maris, duk da kuwa gwamnatin jihar Filato ta haramta taron mutane da suka kai 50 a jihar.

Wannan na zuwa ne bayan kwanaki kadan da Malamin ya kwatanta cutar coronavirus da farfagandar turawan Yamma, kamar yadda shafin Linda Ikeji ya wallafa.

Limamin ya kara da bayyana cewa babu wata hukuma da ta isa ta hana shi ko mabiyansa yin sallar jam'i a masallatai.

Amma kuma Limamin ya sha tsinuwar 'yan Najeriya bayan bidiyonsa da mabiyansa ya bayyana suna cike da Masallaci a garin Jos na jihar Filato.

DUBA WANNAN: Covid-19: Akwai yiwuwar mutum 39,000 su kamu da cutar a Legas - Kwamishinan Lafiya

Idan zamu tuna, tun bayan da cutar coronavirus ta shigo Najeriya ne malamai suka dinga tsokaci tare da yin kira ga mabiyansu a kan su bi duk dokar da gwamnati ta kafa a kan hana yaduwar muguwar cutar.

Wasu manyan fastoci sun yi bauta a ranar Lahadi da ta gabata amma gwamnati ta yi kira garesu akan su kauracewa hada taruka irin haka don gujewa yaduwar cutar.

Amma a yau kwatsam, sai ga Sheikh Sani Yahaya Jingir ya ja sallar Juma'a a jihar Filato duk da kuwa gwamnatin jihar ta haramtawa jama'ar jihar yin taron jama'a da ya kai 50.

Tun kafin nan wani bidiyon malamin ya yawaita a kafar sada zumuntar zamani inda yake cewa babu wanda ya isa ya hanasu ibada don wannan cutar farfagandar turawan yamma ce.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel