Coronavirus: Ina cikin koshin lafiya a killace – Gwamnan Bauchi, Bala Mohammed
Gwamnan jahar Bauchi, Bala Mohammed ya jadadda cewar yana cikin koshin lafiya yayinda aka kebancesa sakamakon kamuwa da ya yi da cutar coronavirus.
A ranar Talata ne dai aka tabbatar da cewa gwamnan na dauke da cutar ta Covid-19 wacce ta mamaye duniya musamman kasashen ketare.
Mohammed ya killace kansa tun bayan da ya yi hannu da dan Atiku Abubakar, tsohon mataimakin shugaban kasa, wanda aka gano yana dauke da cutar.

Asali: Facebook
A sakon da gwamnan ya wallafa a shafinsa na Facebook, Mohammed ya ce yana lafiya kuma har yanzu bai fara nuna wata alama ta cutar ba.
Gwamnan ya kuma yi godiya a kan kulawar da ya samu daga wajen mutane a wannan yanayi da ya tsinci kansa.
Har ila yau Gwamnan ya bayar da tabbacin cewa za a shawo kan wannan annoba da ake ciki da izinin Allah.
Ya ce: "Assalamualaikum. Ina godiya sosai da soyayya da kulawar da na samu a yan kwanakin nan da suka gabata. Har yanzu ina killace karkashin kulawar likita. Sai dai, ina cikin koshin lafiya sannan ban nuna kowace alama ta rashin lafiya ba. Kada mu yi kasa a gwiwa wajen addu’a, za a wuce wannan lokaci ba da jimawa ba."
KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Dino Melaye ya yi rabon abun tsaftace hannu, Vitamin C sannan ya yiwa Najeriya addu’a
Daga karshe gwamnan ya yiwa mutanen jahar Bauch da Najeriya baki daya addu’an samun rahmar Allah da kariya daga cuta, rashin tsaro da kuma talauci.
A gefe daya mun ji cewa Gwamnatin tarayyar Najeriya a ranar Alhamis ta ki yin magana a kan halin da shugaban ma'aikatar fadar shugaban kasa, Abba Kyari ya ke ciki bayan sakamakon gwaji ya nuna cewa yana dauke da kwayar cutar Covid-19.
Ministocin gwamnatin Najeriya biyu sun ki cewa komai game da halin da ya ke ciki a yanzu, Ministan Lafiya, Osagie Ehanire da Ministan Labarai da Al'adu, Lai Mohammed a lokacin da manema labarai suka musu tambayoyi.
Sunce wannan ba batu bane da ya shafi jama'a kamar yadda kowa na da damar ya bar wa kansa batun lafiyarsa.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng