Gwamnan Nasarawa, mataimakinsa da Sarkin Lafiya sun tsira daga Coronavirus

Gwamnan Nasarawa, mataimakinsa da Sarkin Lafiya sun tsira daga Coronavirus

Sakamakon gwajin mugunyar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, Coronavirus da aka gudanar a kan gwamnan jahar Nassarawa, Abdullahi Sule ya tabbatar da cewa gwamnan baya dauke da cutar.

Haka zalika kwakwantcin gwajin da aka gudanar a kan mataimakin gwamnan, Dakta Emmanuel Akabe da kuma Sarkin Lafia, Mai sharia Sidi Bage duk sun tabbatar da babu kwayoyin cutar a tare da mutanen biyu, inji rahoton jaridar Daily Trust.

KU KARANTA: Annobar Corona: Ba zamu dage zaben kananan hukumomi ba – ODIEC

Gwamnan Nasarawa, mataimakinsa da Sarkin Lafiya sun tsira daga Coronavirus
Gwamnan Nasarawa, mataimakinsa da Sarkin Lafiya sun tsira daga Coronavirus
Asali: Facebook

Gwamnan jahar, Abdullahi Sule ne ya bayyana haka a ranar Juma’a yayin da yake ganawa da manema labaru a garin Lafia, inda yace mutumin da ake zargi yana dauke da cutar da ya shigo daga Abuja shi ma ya sha, bayan gwajin cutar ya nuna baya dauke da ita.

Gwamnan ya ce ya dauki matakin killance kansa ne bayan samun labarin wasu mutane da ya yi mu’amala dasu a wajen jahar Nasarawa sun kamu da cutar.

“Daga nan na nemi shawarar kwararru da suka dauki jinina da na mataimaki na da kuma na Sarkin Lafiya domin a gudanar da gwaji. Cikin ikon Allah da sakamakon gwajin ya fito, ya nuna bamu dauke da kwayar cutar.” Inji shi.

Tuni dai gwamnatin jahar Nasarawa ta bada umarnin rufe dukkanin wuraren ibada a duk fadin jahar a matsayin matakin rage yaduwar cutar, haka zalika haramcin ya shafi dukkanin tarukan siyasa, aure ko suna.

Bugu da kari gwamnan ya bada umarnin rufe kasuwanni da shaguna, illa shagunan dake sayar da abinci da kayan magani, amma ya nanata ma jama’an jahar cewa ba’a samu bullar cutar a jahar ba, kawai dai suna daukan matakin kandagarki ne.

A wani labari kuma, sakamakon gwajin da aka gudanar a kan Firai ministan kasar Birtaniyar, Boris Johnson game da annobar cutar Coronavirus, ta nuna shi ma ya kamu da kwayar da cutar.

Haka zalika baya ga Johnson, an kebance sauran ma’aikatan fadar gwamnatin Birtaniyan bisa shawarar babban likitan Ingila, Farfesa Chris Whitty ya bayyana.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitnghausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng