Bidiyon wani mai siyar da kayan gwari da aka kama yana wanke kayan marmari da ruwan kwata

Bidiyon wani mai siyar da kayan gwari da aka kama yana wanke kayan marmari da ruwan kwata

- Wata yar Najeriya da aka ambata da suna Tobi Odukoya ta ja hankalin mutane a kan wasu masu siyar da kayan marmari da ke wanke kayan sana’arsu da ruwan datti na kwata

- Odukoya ta je shafin Twitter domin bayyana fuskokin wasu bayin Allah da ta kama suna aikata haka

- Matar ta wallafa bidiyon a yanar gizo don tabbatar da ikirarinta

Kamar yadda kuka sani mazaje kan shiga harkar siyar da kayan marmari a yankin kudancin Najeriya. Sukan sanya kayan sana’ar nasu a baro suna bin unguwa-unguwa don tallata hajarsu.

Sai dai kwanan nan ne wata yar Najeriya mai suna Tobi Odukoya ta ja hankalin mutane ga wasu masu siyar da kayan marmari a yankin Agungi da ke babbar titin Lekki-Epe.

Odukoya ta je shafin Twitter domin fallasa abunda ta gani yayinda take tuki a hanyar. Matar ta wallafa wani bidiyo a yanar gizo domin tabbatar da ikirarin na ta.

A bidiyon da ta wallafa a yanar gizo, An gano wasu masu siyar da kayan marmari da kayansu. Sai aka gano wani matashi ya duka yana wanke mangoronsa a cikin ruwan datti da ke kwaranya.

A lokacin da ya gano Odukoya tana doso shi, sai ya yi gaggawan matsawa daga wajen kwatan sannan ya tsaya a wajen zamansa. Yayinda matar ke ta zagin mutanen, sai kawai suka tsaya suna kallonta.

Odukoya ta kara gargadin mutane daga yankin Agungi da su guji siyan kayan marmari daga wajen mutanen.

Kalli bidiyon a kasa:

Yan sa’o’i kadan bayan Odukoya ta yi ja hankalin kan masu wanke kayan marmari da ruwan datti na kwatan, sai wani shafin Facebook mai suna NIGERIANS ya bayyana cewa an kama wani mai siyar da kayan marmari a yayinda yake wankewa a ruwan kwata mai wari.

KU KARANTA KUMA: Labari da dumi-dumi: NNPC za ta bayar da gudunmawar $30m domin yaki da coronavirus

Shafin Facebook din ya shawarci mutane da su kula da inda suke siyan kayan marmarinsu.

Kalli bidiyon a kasa:

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel