Coronavirus: Dino Melaye ya yi rabon abun tsaftace hannu, Vitamin C sannan ya yiwa Najeriya addu’a

Coronavirus: Dino Melaye ya yi rabon abun tsaftace hannu, Vitamin C sannan ya yiwa Najeriya addu’a

- A kokarin yakar cutar Coronavirus, Dino Melaye, wani dan siyasar Najeriya ya bayar da gudunmawar kayayyaki da dama irinsu abun tsaftace hannu ga mutane a jahar Kogi

- Dan siyasar na Najeriya ya ce za a raba wa mutane kayayyakin ba tare da la’akari da addini ko akidar siyasar su ba

- Melaye ya kuma kara da yin addu’a yayinda ya roki Allah da ya fitarwa da kasar da mummunan cutar

Shahararren dan siyasar nan na Najeriya, Dino Melaye ya yi bajinta yayinda ya bayar da gudanarwa abun tsaftace hannu da Vitamin C ga mutane a jahar Kogi.

A wani dan gajeren bidiyo da ya yi a shafinsa na Facebook a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris, ya bayyana cewa zai bayar da kayayyakin ba tare da la’akari da addini ko siyasa ba.

Ya ce babu bukatar sanin dan jam’iyyar Peoples Democratic Party ko na All Progressives Congress domin ba za a nuna wa kowa wariya ba.

“Don haka babu PDP babu APC, na kowa ne. Allah zai warkar da kasar mu da sunan Allah,” in ji shi.

A cikin bidiyon An gano kwalayen abun tsaftace hannu da sauran kayayyaki yayinda aka gano shi yana ba wasu maza umurni kan yadda za su yi rabon kayayyakin.

A bangare guda mun ji cewa shugaban hukumar kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari ya sanar da cewa hukumar mai kula da man fetur da iskar gas za ta bayar da gudunmawar dallar Amurka miliyan 30 kimanin Naira biliyan 11,093,719,460.80 ga gwamnatin Najeriya domin yaki da annobar coronavirus a kasar.

Kyari ya yi wannan jawabin ne a babban birnin tarayya Abuja a wurin taron manema labarai da ake gudarwa a halin yanzu kamar yadda jaridar New Telegraph ta ruwaito.

Attajirai da 'yan kasuwa da dama a duniya da ma Najeriya sun bayar da ta su gudunmawar domin taimakawa kasar cin galaba kan yaki da ta ke yi da cutar.

Cikin wadanda suka bayar da gudunmawar kudade akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Alhaji Aliko Dangote, Attajirin dan kasuwar kasar China, Jack Ma, Shugaban kamfanin BUA da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel