Labari da dumi-dumi: NNPC za ta bayar da gudunmawar $30m domin yaki da coronavirus

Labari da dumi-dumi: NNPC za ta bayar da gudunmawar $30m domin yaki da coronavirus

Shugaban hukumar kamfanin man fetur na Najeriya (NNPC), Mele Kyari ya sanar da cewa hukumar mai kula da man fetur da iskar gas za ta bayar da gudunmawar dallar Amurka miliyan 30 kimanin Naira biliyan 11,093,719,460.80 ga gwamnatin Najeriya domin yaki da annobar coronavirus a kasar.

Kyari ya yi wannan jawabin ne a babban birnin tarayya Abuja a wurin taron manema labarai da ake gudarwa a halin yanzu kamar yadda jaridar New Telegraph ta ruwaito.

Ya ce, "Muna sanar da cewa a karo na farko za mu bayar da kudi dallar miliyan 30 a matsayin tallafi domin yaki da kayar cutar Covid-19 a Najeriya.

"Wannan gudunmawar za a bayar da shi ne ga gwamnatin tarayya a yunkurin da ta ke yi na takaita yaduwa da kawo karshen annobar Covid-19 a kasar.

Labari da dumi-dumi: NNPC za ta bayar da gudunmawar $30m domin yaki da coronavirus

Labari da dumi-dumi: NNPC za ta bayar da gudunmawar $30m domin yaki da coronavirus
Source: Twitter

DUBA WANNAN: Yanzu-yanzu: Sakamakon gwajin Coronavirus da aka yi wa Lai Mohammed da Akeredolu ya fito

"Da wannan gudunmar da ma'aikatar ta bayar, za mu samar da kayan aikin asibiti, zirga-zirga da tallafawa masu jinya da kuma samar da kayayyakin da asibitoci ke bukata da za a dade ana amfani da su a kasar."

Attajirai da 'yan kasuwa da dama a duniya da ma Najeriya sun bayar da ta su gudunmawar domin taimakawa kasar cin galaba kan yaki da ta ke yi da cutar.

Cikin wadanda suka bayar da gudunmawar kudade akwai tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, Alhaji Aliko Dangote, Attajirin dan kasuwar kasar China, Jack Ma, Shugaban kamfanin BUA da sauransu.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Tags:
Online view pixel