Gwamnatin jahar Gombe ta rufe iyakokinta saboda coronavirus

Gwamnatin jahar Gombe ta rufe iyakokinta saboda coronavirus

- Gwamnatin jahar Gombe ta sanar da rufe iyakokinta a kokarinta na hana yaduwar cutar coronavirus a jahar

- Gwamna Inuwa Yahaya, ya ce sun dauki matakin ne domin gudun 'yan jahar tasa su kwaso cutar daga wasu wurare ko kuma masu dauke da cutar su shigar da annobar jahar

- Jahar ta Gombe dai ba ta da ko da mutum daya da ke dauke da wannan cuta

Gwamnatin jahar Gombe karkashin jagorancin Gwamna Muhammad Inuwa Yahaya, ta sanar da rufe iyakokinta duk a kokarinta na daukar matakin hana yaduwar annobar coronavirus zuwa cikin jahar.

A wani jawabi ga manema labarai gwamna Inuwa Yahaya, ya ce sun dauki matakin ne domin gudun 'yan jahar tasa su kwaso cutar daga wasu wurare ko kuma masu dauke da cutar su shigar da annobar jahar.

Gwamnatin jahar Gombe ta rufe iyakokinta saboda coronavirus
Gwamnatin jahar Gombe ta rufe iyakokinta saboda coronavirus
Asali: UGC

Jahar ta Gombe dai ba ta da ko da mutum daya da ke dauke da wannan cuta, amma gwamnan ya ce yin rigakafi ne kawai zai hana annobar shiga jihar.

Gombe ce jiha ta uku a jerin jihohin da suka rufe iyakokinsu bayan jihohin Kano da Kaduna.

KU KARANTA KUMA: Covid-19: Buhari ya jinjina wa Elumelu, Rabiu, Dangote, Atiku da sauransu kan gudunmawar da suka bayar

A gefe guda mun ji cewa Gwamnatin jahar Katsina ta sanar da daukan matakin dakatar da sallar Juma’a tare da tarukan bautan mabiya addinin kirista a coci coci, a wani mataki na kandagarki domin kauce ma yaduwar annobar cutar nan mai toshe numfashin dan Adam, Coronavirus.

Kwamishinan watsa labaru na jahar, Abdulkarim Sirikam ne ya bayyana haka cikin wata sanarwa daya raba ma manema labaru a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris inda yace duk wani taron daurin aure ko na siyasa sun haramta a wannan lokaci.

Don haka yace gwamnati na shawartar jama’a su takaita ire iren tarukan nan kamar yadda hukumar kiyaye yaduwar cututtuka ta kasa, NCDC, ta umarta duba da yadda cutar Coonavirus ke cigaba da yaduwa a kasar.

“Haka zalika gwamnati na kira ga jama’a su yi biyayya ga wannan sabon umarni, sa’annan su cigaba da yi ma kasa addua game da wannan mugunyar jarabawa da duniya ke fama da ita.” Inji kwamishina Abdulkarim.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel