Kasar Iran ta samu karin mutane 144 da suka mutu sakamakon coronavirus, jimlar mutane 2,378 kenan suka mutu

Kasar Iran ta samu karin mutane 144 da suka mutu sakamakon coronavirus, jimlar mutane 2,378 kenan suka mutu

- Iran a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris, ta sanar da sabbin mutane 144 da suka mutu daga cutar coronavirus

- A yanzu haka jimlar wadanda suka mutu sakamakon annobar ta covid -19 a kasar ya kama 2,378

- Kakakin ministan lafiya na kasar Kianoush Jahanpour, ya ce gaba daya an samu mutane 32,332 da ke dauke da cutar a kasar

Kasar Iran a ranar Juma’a, 27 ga watan Maris, ta sanar da sabbin mutane 144 da suka mutu daga cutar coronavirus, inda jimlar wadanda suka mutu ya kama 2,378 a wannan annoba da ya karade duniya.

“A cikin sa’o’i 24 da suka gabata, mun samu sabbin mutane 2,926 da suka kamu da cutar coronavirus a fadin kasar,” in ji kakakin ministan lafiya na kasar Kianoush Jahanpour.

Kasar Iran ta samu karin mutane 144 da suka mutu sakamakon coronavirus, jimlar mutane 2,378 kenan suka mutu
Kasar Iran ta samu karin mutane 144 da suka mutu sakamakon coronavirus, jimlar mutane 2,378 kenan suka mutu
Asali: UGC

Ya kara da cewa: “Hakan na nufin gaba daya mun samu mutane 32,332 da ke dauke da cutar.”

Daga karshe ya bayyana cewa zuwa yanzu mutane 11,133 daga cikin wadanda aka kwantar sun farfado.

KU KARANTA KUMA: Amurka ta fi China yawan wadanda suka kamu da coronavirus

A gefe daya mun ji cewa kasar Afirka ta Kudu ta rasa mutane biyu a karo na farko sakamakon cutar ta covid-19.

Ministan lafiya na kasar, Zwelini Mkhize ne ya sanar da hakan a ranar Juma'a, 27 ga watan Maris inda ya kara da cewa mutane biyun da suka mutu duk sun fito ne daga lardin Yammacin Cape, inda daya ya mutu a asibitin kudi yayinda na biyun kuma a asibitin gwamnati.

Ya kara da cewa ya zuwa yanzu yawan mutanen da suka kamu sun wuce 1,000, inda ya ce nan gaba kadan za a bayar da kididdiga.

Hakan na zuwa ne a dai-dai lokacin da kasar ta aiwatar da dokar kulle ta kwana 21 a ranar Juma'a domin hana yaduwar cutar coronavirus.

Tuni dai jami'an tsaron kasar suka fara shawagi don ganin jama'a na martaba dokar rufe kasar da aka dauka ta ba shiga ba fita har tsawon makwanni uku aiwatar da dokar rufe makwanni uku.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel