Cutar Coronavirus ta jefa Gwamnatin kasar Kosovo cikin halin ha’ula’i

Cutar Coronavirus ta jefa Gwamnatin kasar Kosovo cikin halin ha’ula’i

Mun ji cewa Firayim Ministan kasar Kosovo Albin Kurti ya na cikin mawuyacin hali bayan da aka fara nunawa gwamnatinsa cewa ta gaza kuma ba za ta iya kai labari ba.

Kamar yadda rahotanni su ka bayyana daga hukumar dillacin labarai na kasa, manyan shugabannin Kosovo uku sun samu kansu cikin sabani a daidai lokacin annobar.

Shugaban ‘Yan adawa Isa Mustafa na jam’iyyar LDK ne ya kawo maganar kada kuri’ar nuna rashin amincewa a majalisar Kosovo ga gwamnatin shugaban kasa Albin Kurti.

Albin Kurti ya dare kan mulki ne a karkashin jam’iyyar kasa ta VV ‘yan kwanaki kadan da su ka wuce. Sai dai kafin a kai ko ina kujerar Firayim Ministar ta fara tangal-tangal.

Albin Kurti ya hada kai da Isa Mustafa ne wajen samun kujerar Firayim Minista a zaben bara. Watanni kadan bayan ya dare kan mulki, ‘Yan siyasar su ka fara samu matsala.

KU KARANTA: Gwamnan Najeriya ya ce ba zai kebewa jama'a saboda tsoron Coronavirus ba

Cutar Coronavirus ta jefa Gwamnatin kasar Kosovo cikin halin ha’ula’i

Akwai yiwuwar a tsige Albin Kurti a kasar Kosovo
Source: Getty Images

Sabanin shugabannin ya kai intaha ne bayan da Albin Kurti ya ki amincewa da shawarar da shugaban kasa Mista Hashim Thaci ya kawo na yakar cutar Coronavirus a Kosovo.

Hashim Thaci ya bukaci gwamnatin Kurti ta yi maza ta sa dokar ta-baci a Kosovo domin takaikata yaduwar wannan cuta, abin da Firayim Ministan bai yi na’am da shi ba.

Ministan harkokin cikin gidan kasar, Agim Veliu, ya soki matakin da Firayim Ministan ya dauka. Wannan ya sa Kurti ya yi maza ya tsige shi daga kujerar Ministan Gwamnatinsa.

Bayan ganin wannan abu da ya faru tsakanin tsohon Ministan da Firayim Ministan ne Isa Mustafa ya fara huro wuta na ganin an kadawa shugaban kuri’ar rashin amincewa.

Yadda za ayi maganin wannan annoba ya raba kan Kurti da Thaci. Jam’iyyar PDK da LDK sun juyawa Kurti baya inda ita kuma Cutar COVID-19 ta kashe mutum guda kwanaki.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel