Za a shiga matsanancin rashin man fetur yayin da direbobin tanka suka dakata da aiki

Za a shiga matsanancin rashin man fetur yayin da direbobin tanka suka dakata da aiki

Matsalar man fetur ka iya shigowa Najeriya mako mai zuwa bayan direbobin tankar mai sun yanke shawarar dakatawa da aiki saboda cutar Corona da ta addabi duniya baki daya

Kungiyar direbobin tankar man ta kasa baki daya (NARTO), ta bayyana hakane a wata sanarwa da shugaban kungiyar ya fitar, Alhaji Yusuf Othman, a ranar Laraba, inda yayi barazanar cewa mambobin kungiyar za su dakata da aiki har sai lokacin da matsalar Coronavirus ta zo karshe.

Ya ce: "Wannan abu da zamu yi ya zama dole, ganin cewa wuraren da muke dauko kaya wurare ne dake dauke da mutane masu yawa da akalla za a samu mutum 500 a kowanne wuri."

Za a shiga matsanancin rashin man fetur yayin da direbobin tanka suka dakata da aiki

Za a shiga matsanancin rashin man fetur yayin da direbobin tanka suka dakata da aiki
Source: Depositphotos

Othman ya ce direbobin su kwantar da hankalinsu domin kuwa shugabannin kungiyar za su yi iya yinsu wajen basu goyon baya a wannan lokaci.

A daya bangaren kuma an fara ganin jerin gwanon ababen hawa a gidajen mai dake birnin Abuja da kewaye yayin da wasu gidajen man suka daina aiki.

Wakilin Daily Trust ya gano cewa an rufe gidajen mai da yawa a yankin Asokoro ciki kuwa hadda MRS da A.A. Rano.

KU KARANTA: COVID-19: Mazauna Legas na tururuwar siyan Dogonyaro da Tagairi a matsayin magani

Haka kuma a yankin Nyanya, gidajen mai irinsu Sani Brothers da Azman suma sun dakata da sayar da man fetur din.

Haka wasu gidajen mai dake jihar Nasarawa suma sun dakata da sayar da man fetur din.

Gidajen mai irinsu A.A.Rano, AYM SHafa, a Nyanya da kuma Mararraba dake Abuja suna bayar da mai amma kuma layi yayi yawa a wajen.

Haka a yankin Jabi dake Abuja, suma gidan man NIPCO suna sayar da mai amma kuma layi yayi yawa sosai a yankin.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel