Coronavirus: Buhari yana nan yana aiki don kare yan Najeriya - Fadar shugaban kasa

Coronavirus: Buhari yana nan yana aiki don kare yan Najeriya - Fadar shugaban kasa

Fadar shugaban kasa a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris, ta bayar da tabbacin cewa Shugaban kasa Muhammadu Buhari na aiki ba ji ba gani domin tsiratar da yan Najeriya daga annobar Coronavirus.

Mai magana da yawun shugaban kasa, Mista Femi Adesina a wani rubutu da ya wallafa a shafin Twitter ya kuma caccaki wasu mutane wanda ya zarga da yada labaran karya da na mugunta.

A rubutu, Adesina ya ce cutar zuciya da rashin tunani mai kyau na damun masu yada karya da mugun alkaba’i.

Coronavirus: Buhari yana nan yana aiki don kare yan Najeriya - Fadar shugaban kasa

Coronavirus: Buhari yana nan yana aiki don kare yan Najeriya - Fadar shugaban kasa
Source: Depositphotos

Koda dai kakakin shugaban kasar bai ambaci sunayen wadanda yake yiwa hannunka mai sanda ba ko ainahin laifin da suka aikata, akwai alamun cewa yana martani ne ga faifai murya da ke yawo a soshiyal midiya cewa an fitar da shugaba Muhammadu Buhari da Abba Kyari kasar waje domin ganin likita.

Wata mata da ba a bayyana ko wacece ba ta yi ikirarin cewa tana da wata kawa wacce mijinta matukin jirgin saman soji ne kuma cewa an nemi ya fitar da Shugaban kasa da shugaban ma’aikatansa amma ya kasa saboda yana killace kansa saboda kwanan nan ya dawo daga Dubai.

KU KARANTA KUMA: Masu yi da gaske: Abdul Samad Isyaka Rabiu ya bayar da kyautar naira biliyan 1 don yaki da COVID-19

Matar ta yi ikirarin cewa wani matukin jirgin ne ya fitar da Buhari da Kyari wajen kasar.

A gefe guda mun ji cewa Gwamnatin jihar Jigawa, a ranar Alhamis ta sanar da cewa ta rufe iyakokin ta na kasa da jihar Bauchi da ta ke makwabtaka da ita da wasu jihohin bayan an samu bullar cutar da coronavirus a jihar.

Kwamishinan Lafiya na jihar, Abba Zakari ne ya shaidawa manema labarai hakan inda ya ce dokar za ta fara aiki daga ranar Juma'a 27 ga watan Maris.

Mista Zakari ya ce jihar ta tuntubi dukkan masu ruwa da tsaki a fanin da suka hada da kungiyar direbobi na kasa (NURTW) domin tabbatar da cewa kowa ya bi dokar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel