Coronavirus: Babu bukatar in killace kai na inji Hope Uzodinma

Coronavirus: Babu bukatar in killace kai na inji Hope Uzodinma

Mai girma gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya ce ba ya bukatar ya killace kansa daga jama’a a kan cutar Coronavirus da ta ke neman zama annoba a Najeriya.

Gwamnan na Imo ya yi wannan jawabi ne ta bakin Kwamishinansa na yada labarai da tsare-tsare, Declan Emelumba lokacin da fayyace shirin da su ke yi a yanzu.

Gwamnatin Hope Uzodinma ta kuma umarci kwamitin kula da cutar COVID-19 da ke karkashin Farfesa Maurice Iwu da ta dage da kokarin wajen hana yaduwar cutar.

Maurice Iwu wanda ya kware a harkar kera magunguna a Duniya shi ne ke jagorantar wani kwamiti da Hope Uzodinma ya kafa domin yakar cutar Coronavirus a jihar.

A cewar gwamnan, an ba kwamitin duk wasu kayan aikin da su ke bukata domin hana wannan cuta sakat a Imo Daga ciki har da motocin musamman na kar-ta-kwana.

KU KARANTA: Japan ta ba Najeriya gudumuwar kudi na yaki da Coronavirus

Coronavirus: Babu bukatar in killace kai na inji Hope Uzodinma
Uzodinma ya na cikin wadanda su ka hadu da Abba Kyari a taron APC
Asali: Facebook

Gwamnatin Imo ta saye motoci har 27 ne da za a rabawa kowace karamar hukuma. Wadannan motoci za su taimaka da jinya idan aka samu masu cutar COVID-19.

Ko da gwamnan ya na cikin wadanda su ka gana da Malam Abba Kyari a wajen taron jam’iyyar APC a makonnin da su ka gabata, ya nuna cewa ba zai boye kansa ba.

Shugban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, ya na cikin wadanda aka tabbatar cewa sun kamu da COVID-19 a Najeriya, kuma ya hadu da Gwamnonin APC.

Gwamna Uzodinma ya kuma jawo hankalin jama’a cewa da su daina tada hankalinsu, ko kuma su rika yada labaran bogi game da annobar, wanda za su iya tada hankali.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel