Yanzu Yanzu: Sakamakon gwaji ya nuna Gwamna Obaseki baya dauke da coronavirus

Yanzu Yanzu: Sakamakon gwaji ya nuna Gwamna Obaseki baya dauke da coronavirus

- Sakamakon gwaji ya nuna gwamnan jahar Edo, Mista Godwin Obaseki baya dauke da cutar coronavirus

- Sai dai kuma Obaseki ya yanke shawarar ci gaba da killace kansa har zuwa lokacin da za a samu sakamakon gwaji na PCR

- Hadimin gwamnan, Crusoe Osagie ne ya tabbatar da lamarin

Sakamakon gwaji da aka yiwa gwamnan jahar Edo, Mista Godwin Obaseki ya nuna baya dauke da cutar coronavirus, amma ya yanke shawarar ci gaba da killace kansa.

A wani jawabi daga mai bashi shawara na musamman kan shafukan labarai, Mista Crusoe Osagie, ya ce sakamakon ya kasance na gwajin lafiya na gaggawa ne, yayinda gwamnan ke jiran sakamakon gwajin PCR.

Yanzu Yanzu: Sakamakon gwaji ya nuna Gwamna Obaseki baya dauke da coronavirus

Yanzu Yanzu: Sakamakon gwaji ya nuna Gwamna Obaseki baya dauke da coronavirus
Source: Depositphotos

A cewarsa: “Zan iya tabbatar da cewar gwamnan baya dauke da cutar coronavirus a lokacin da ya yi gwajin lafiya gaggawa a yanzu yana jiran karin sakamako na PCR.

“A wannan dan lokacin, gwamnan ya yanke shawarar ci gaba da aiki a matakin killace kai kuma baya jin kowani alamu na kamuwa.”

KU KARANTA KUMA: Coronavirus ta sa wata tsohuwa 'Yar Kano ta yi shahada a Amurka

A gefe daya mun ji cewa Ministoci takwas ne da suka hada da mace daya tare da wasu manyan jami'an gwamnati ne a ranar Laraba aka dauka jininsu don gwajin cutar COVID-19.

Akwai karin ministocin da za a gwada bayan sakamakon wadannan ya fito. Ana tsammanin fitowar sakamakon a yau Alhamis.

An gano cewa, wasu daga cikin ministocin da ke da alhakin shugabantar bangaren kula da annobar COVID-19 ne a kasar nan aka fara gwadawa.

An gano cewa an diba jinin ministocin ne daga hukumar hana yaduwar cutuka ta kasa ta NCDC.

Duk da cewa an ki bayyana sunayen ministocin, za a sanar dasu sakamakonsu a yau Alhamis, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Wata majiya mai karfi ta ce "Matakin dai na kariya ne tunda wadanda aka gwada din suna kan taka rawar gani wajen taimakon kasar nan a yayin da take fuskantar kalubalen annobar COVID-19."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel