Coronavirus ta sa wata tsohuwa 'Yar Kano ta yi shahada a Amurka

Coronavirus ta sa wata tsohuwa 'Yar Kano ta yi shahada a Amurka

- Allah ya yiwa wata ‘yar asalin jahar Kano da ke zama a Amurka mai suna, Hajia Laila Abubakar Ali rasuwa

- Tsohuwar mai shekara 60 ta rasu ne bayan ta kamu da cutar coronavirus

- Ta kasance yayar sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin addini na Kano

Rahotanni da ke zuwa mana ya nuna cewar Allah ya yiwa wata ‘yar asalin jahar Kano da ke zama a Amurka mai suna, Hajia Laila Abubakar Ali rasuwa.

Tsohuwar mai shekara 60 ta rasu ne bayan ta kamu da cutar coronavirus.

Kakakin gwamna Abdullahi Umar Ganduje na jahar Kano, Salihu Yakasai ne ya bayyana hakan a ranar Alhamis, 26 ga watan Maris.

Coronavirus ta sa wata tsohuwa 'Yar Kano ta yi shahada a Amurka
Coronavirus ta sa wata tsohuwa 'Yar Kano ta yi shahada a Amurka
Asali: Facebook

A wani rubutu da ya wallafa a twitter, ya bayyana cewar marigayiyar ta kasance yayar sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin addini na Kano.

Ya wallafa: “Wata ‘yar asalin Kano da ke zama Amurka mai suna Hajia Laila Abubakar Ali ta mutu sakamakon cutar Covid-19. Tsohuwar mai shekara 60 ta mutu a jiya bayan ta kamu. Ta kasance yayar sakataren din-din-din na ma’aikatar harkokin addini na Kano. Allah ya ji kanta da rahma.”

KU KARANTA KUMA: A Kaduna, Kano, Ogun, Taraba, Yobe, Gwamnoni su na cigaba da zuwa ofis

A bangare guda mun ji cewa an rufe majalisar wakilan tarayya da kuma ta dattawa a Najeriya, a sakamakon cutar Coronavirus da ta shigo Najeriya, har ta yi sanadiyyar mutuwar wani.

A Ranar 25 ga Watan Maris, Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa an rufe majalisun tarayyar domin a hana yaduwar cutar COVID-19 da ta shiga kasashe fiye da 190.

Shugaban majalisar dattawa watau Dr. Ahmad Ibrahim Lawan ya bada wannan sanarwa bayan wani zama da su ka yi na kusan sa’a guda a Ranar Talatar nan da ta gabata.

Ahmad Lawan ya ce Sanatoci sun dakatar da aiki a majalisar, sai dai a cewarsa, za su tsaya jiran aikin ko-ta-kwana a Abuja, su dawo bakin aiki idan akwai bukatar gaggawa.

Lawan ya ce Sanatocin za su tafi hutun makonni biyu, za su dawo bakin aiki a Ranar 7 ga Watan Afrilu. Lawan ya yi kira ga gwamnati ta dage wajen yakar wannan cuta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel