COVID-19: Ministoci 8 ke cikin fargaba, suna jiran sakamakon gwaji

COVID-19: Ministoci 8 ke cikin fargaba, suna jiran sakamakon gwaji

- Ministoci takwas ne da suka hada da mace daya tare da wasu manyan jami'an gwamnati ne a ranar Laraba aka dauka jininsu don gwajin cutar COVID-19

- Akwai karin ministocin da za a gwada bayan sakamakon wadannan ya fito. Ana tsammanin fitowar sakamakon a yau Alhamis

- Matakin dai na kariya ne tunda wadanda aka gwada din suna kan taka rawar gani wajen taimakon kasar nan a yayin da take fuskantar kalubalen annobar

Ministoci takwas ne da suka hada da mace daya tare da wasu manyan jami'an gwamnati ne a ranar Laraba aka dauka jininsu don gwajin cutar COVID-19.

Akwai karin ministocin da za a gwada bayan sakamakon wadannan ya fito. Ana tsammanin fitowar sakamakon a yau Alhamis.

An gano cewa, wasu daga cikin ministocin da ke da alhakin shugabantar bangaren kula da annobar COVID-19 ne a kasar nan aka fara gwadawa.

An gano cewa an diba jinin ministocin ne daga hukumar hana yaduwar cutuka ta kasa ta NCDC.

Duk da cewa an ki bayyana sunayen ministocin, za a sanar dasu sakamakonsu a yau Alhamis, kamar yadda jaridar The Nation ta ruwaito.

Wata majiya mai karfi ta ce "Matakin dai na kariya ne tunda wadanda aka gwada din suna kan taka rawar gani wajen taimakon kasar nan a yayin da take fuskantar kalubalen annobar COVID-19."

COVID-19: Ministoci 8 ke cikin fargaba, suna jiran sakamakon gwaji
COVID-19: Ministoci 8 ke cikin fargaba, suna jiran sakamakon gwaji
Asali: Facebook

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: Abba Kyari ya isa asibitin Gwagwalada don fara magance cutar COVID-19

Majiyar ta kara da cewa: "Wannan gwamnatin na da adalci kuma tana kokari wajen kokarin shawo kan annobar COVID-19. A halin yanzu ministoci takwas ne aka diba jininsu tare da wasu manyan jami'an gwamnati don gwajin cutar. Wannan gwamnatin bata da abin boyewa, a shirye take ta bayyana komai kamar yadda kasashen duniya ke yi.

"Amfanin gwajin shine don tabbatar da cewa masu kokarin shawo kan annobar na da isasshiyar lafiya. Inda suke bukatar kula, gwamnati za ta dauka matakan da suka dace.

"Muna son 'yan Najeriya su tabbatar da cewa annobar ba ta bin launin fata ko siyasa. COVID-19 cuta ce da bata san iyakoki ba kuma bata san komai game da kudi ko talauci ba."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel