Coronavirus: Gwamna Obaseki ya shiga killace kansa

Coronavirus: Gwamna Obaseki ya shiga killace kansa

- Gwamna Godwin Obaseki ya shiga killace kansa

- Hadimin Obaseki kan labarai, Crusoe Osagie ne ya bayyana hakan a ranar Laraba, 25 ga watan Maris

- Gwamnan ya halarci taron ganawa da Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Shugaban ma’aikatar shugaba Muhammadu Buhari, Abba Kyari

Biyo bayan halartan taron kungiyar gwamnonin Najeriya da na tattalin arziki na kasa, Gwamna Godwin Obaseki ya shiga killace kansa.

A wani jawabi da aka saki a ranar Laraba, 25 ga watan Maris daga hadimin Obaseki, Crusoe Osagie, ya bayyana cewa Gwamna Bala Mohammed na Bauchi da Abba Kyari, Shugaban ma’aikatan Shugaban kasa Muhammadu Buhari, wadanda ke dauke da cutar coronavirus duk sun halarci taron.

Coronavirus: Gwamna Obaseki ya shiga killace kansa

Coronavirus: Gwamna Obaseki ya shiga killace kansa
Source: Depositphotos

Sai dai kuma, Osagie bai fayyace cewar ko Obaseki ya fara ganin alamu na cutar ba, jaridar The Nation ta ruwaito.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Likita dan shekara 26 ya mutu bayan ya sadaukar da lokaci yana taimakon wadanda suka kamu

A gefe guda mun ji cewa gwamnan Bauchi, Sanata Bala Abdulkadir Mohammed ya na cikin wadanda aka tabbatar cewa sun kamu da cutar nan ta Coronavirus a Najeriya.

Wani daga cikin Hadiman Gwamnan, Mukhtar Gidado, ya fito ya bayyana cewa Mai gidan na sa ya kamu da cutar ne bayan ya hadu da Mohammed Atiku Abubakar.

Mukhtar Gidado ya fitar da jawabi jiya ya na cewa Bala Abdulkadir Mohammed ya gaisa da ‘Dan tsohon mataimakin shugaban kasar, har kuma sun yi musafaha.

Sai dai kuma yanzu rahotanni sun zo mana cewa Alhaji Mohammed Atiku Abubakar, ya karyata wannan jawabi da ya fito daga gidan gwamnatin na jihar Bauchi.

Yaron tsohon mataimakin shugaban Najeriyar ya musanya zargin cewa ya mikawa Gwamnan hannu, a cewarsa gaisawa kurum su ka yi ba tare da musafaha ba.

Atiku Abubakar ya bayyana wannan ne a wani sako da ya aikawa gidan Jaridar Premium Times, bayan Manema labarai sun bukaci jin ta bakinsa game da lamarin.

Maras lafiyan ya nuna cewa sun zaune ne tare da Iyalansu a gefe daban-daban na jirgin saman da ya dauko su tare da Tawagar gwamnan daga Legas zuwa Abuja.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng News

Online view pixel