Coronavirus: Likita dan shekara 26 ya mutu bayan ya sadaukar da lokaci yana taimakon wadanda suka kamu

Coronavirus: Likita dan shekara 26 ya mutu bayan ya sadaukar da lokaci yana taimakon wadanda suka kamu

- Wani matashin likita, wanda ke da shekara 26 a duniya, ya sadaukar da rayuwarsa yayin taimaka wa marasa lafiyan da suka kamu da cutar coronavirus

- An tattaro cewa likitan mai suna Dr Usama Riaz, ya shafe lokacinsa yana tantancewa da kula da masu cutar Cocid-19

- Likitan ya kamu ne a yanayin sannan ya rasa ransa a kan haka

Wani likita mai suna Usaman Riaz ya kasance daya daga cikin jami’an lafiya da suka sadaukar da kansu wajen kula da wadanda suka kamu da cutar coronavirus a fadin duniya.

Likitan wanda ya sadaukar da lokacinsa da karfinsa wajen yaki don ceto mutane daga annobar da ya haifar da rudani a fadin duniya, ya kasance dan shekara 26 a lokacin da ya mutu.

Wani mai amfani da shafin twitter @_SJPeace_, ne ya sanar da mutuwarsa sannan ya bayyana yadda Riaz ya kamu da cutar a kokarinsa na isar da aikinsa.

“Wannan shine Dr Usama Riaz. Ya shafe yan makonnin da suka gabata wajen tantancewa da kula da marasa lafiyan da suka kamu da cutar coronavirus a Pakistan. Ya san cewa babu magani. Ya jajairce.

KU KARANTA KUMA: Hotunan wasu yan gida daya su 4 da suka mutu a cikin barci

“A yau ya rasa nasa rayuwar sakamakon cutar coronavirius amma ya ba mutane rayuwa da karfafa wa wasu da dama gwiwa. Ku san sunansa,” in ji mai amfani da shafin na twitter.

A wani labari na daban, mun ji cewa ma'aikatan ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban, Abba Kyari, guda uku sun kamu da cutar Coronavirus (COVID-19).

An yi yunkurin ji daga bakin masu magana da yawun shugaban kasa amma ba a samu nasara ba saboda gaba daya ba a ga Garba Shehu da Femi Adesina a fadar ba.

Majiya daga fadar shugaban kasan wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya tabbatar da cewa an shawarci dukkan mutanen da suka yi hulda da Abba Kyari.

Ya ce ana kyautata zaton cewa hakan yasa ma'aikatan fadar shugaban kasa basu zo aiki yau ba. Bugu da kari, dukkan ma'aikatan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, basu shiga fadar ba a yau illa mai magana da yawunsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Nigeria

Online view pixel