Hotunan wasu yan gida daya su 4 da suka mutu a cikin barci

Hotunan wasu yan gida daya su 4 da suka mutu a cikin barci

- Wasu iyalai yan Najeriya su hudu sun mutu a cikin baccinsu

- An tattaro cewa ma’auratan tare da yaransu biyu sun mutu a ranar 22 ga watan Maris

- Wata mai suna Nkiru Chukwuemeka Unachukwu ce ta sanar da labarin a shafin Facebook

Yayinda yan Najeriya ke ci gaba da gwagwarmaya da annobar da ake ciki a yanzu, abubuwan bakin ciki na ci gaba da faruwa a fadin kasar. Kwanan nan ne aka rahoto cewa wasu iyalai su hudu sun mutu a cikin barcinsu.

Wata mai amfani da shafin Facebook, Nkiru Chukwuemeka Unachukwu ce ta watsa labarin.

Iyalan wadanda suka hada da ma’auratan da yaransu kanana su biyu, sun kwanta barci ne inda basu kara tashi ba. An dauki hoton gawarwakin iyalan a kan gado, a yanayin da suka kwanta barcin, illa gawar mahaifin wanda rabin cikinsa na a kan gado sannan rabi na a kasa.

“Na kasa yarda ta yaya za a yi iyalai guda ba tare da ciwon komai ba a ce miji, mata da yara biyu su kwanta barci a daren jiya amma su kasa tashi da safe. Akwai hannun shaidan a ciki. Allah ya ji kanku,” Unachukwu ta rubuta.

KU KARANT KUMA: Coronavirus: Sakamakon gwaji ya nuna mutane 3 da aka killace a Kaduna basa dauke da cutar

A wani labari na daban, mun ji cewa ma'aikatan ofishin shugaban ma'aikatan fadar shugaban, Abba Kyari, guda uku sun kamu da cutar Coronavirus (COVID-19).

An yi yunkurin ji daga bakin masu magana da yawun shugaban kasa amma ba a samu nasara ba saboda gaba daya ba a ga Garba Shehu da Femi Adesina a fadar ba.

Majiya daga fadar shugaban kasan wanda ya bukaci a sakaye sunansa ya tabbatar da cewa an shawarci dukkan mutanen da suka yi hulda da Abba Kyari.

Ya ce ana kyautata zaton cewa hakan yasa ma'aikatan fadar shugaban kasa basu zo aiki yau ba. Bugu da kari, dukkan ma'aikatan mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, basu shiga fadar ba a yau illa mai magana da yawunsa.

A yanzu dai, da alamun ana shirin kulle fadar shugaban kasar saboda an umurci dukkan dukkan ma'aikatan su koma gida.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel