Coronavirus: Sakamakon gwaji ya nuna mutane 3 da aka killace a Kaduna basa dauke da cutar

Coronavirus: Sakamakon gwaji ya nuna mutane 3 da aka killace a Kaduna basa dauke da cutar

- Sakamakon gwajin cutar coronavirus da aka yiwa wasu mazauna Kaduna su uku wadanda aka killace bayan ya bayyana cewar sun je kasashen Ingila da Masar ta fit0

- Sakamakon ta nuna basa dauke da cutar ta COVID-19

- Hakan na nufin babu wanda ke dauke da coronavirus a Kaduna kamar yadda gwamnatin jahar ta bayyana

Sakamakon gwajin da aka yiwa wasu mazauna Kaduna su uku wadanda aka killace bayan ya bayyana cewar sun je kasashen Ingila da Masar, ta nuna basa dauke da cutar coronavirus kamar yadda gwamnatin jahar ta sanar a ranar Talata.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa kwamishinar lafiya ta jahar Kaduna, Dr. Amina Mohammed-Baloni a ranar Asabar ta bayyana cewa an daura wasu mazauna Kaduna uku da suka dawo daga kasashen Ingila da Masar a matakin killace kai sannan ana ta lura da su kan cutar duk da cewar ba su nuna alamun kamuwa ba.

Coronavirus: Sakamakon gwaji ya nuna mutane 3 da aka killace a Kaduna basa dauke da cutar

Coronavirus: Sakamakon gwaji ya nuna mutane 3 da aka killace a Kaduna basa dauke da cutar
Source: Twitter

Sai dai kuma Baloni a ranar Talata ta ce jahar ta samu sakamakon gwajin mutanen guda uku wanda ya nuna cewa basa dauke da cutar ta coronavirus, “hakan na nufin babu wanda ke dauke da coronavirus a Kaduna.”

Kwamishinar yayinda ta ke zantawa da manema labarai, ta ce an tanadi kayayyaki na musamman a cibiyar kula da cutar domin shirin ko ta kwana.

KU KARANTA KUMA: Masu dauke da coronavirus yanzu a Najeriya sun kai 46 yayinda NCDC ta tabbatar da sabbin mutane 2

A bangare guda mun ji cewa Gwamnan jihar Plateau Simon Lalong ya bayar da umurnin ma'aikatan gwamnati masu mataki na daya zuwa 12 a jihar su fara yin aiki daga gidajensu sannan kuma a rufe kasuwanni.

Dokar za ta fara aiki daga ranar Laraba 25 ga watan Maris kamar yadda Channels TV ta ruwaito.

An dauki matakin ne yayin taron gaggawa da majalisar zartarwa na jihar ta yi domin kare yaduwar annobar kwayar cutar Covid-19 da ke kisa ba kakautawa.

Dokar kuma ta ce dukkan masu wuraren shakatawa kamar kulob da mashaya su ma su rufe daga ranar 25 ga wtaan Maris na 2020. Masu sayar da abinci kuma su rika kai wa kwastomominsu abincin gida domin hana cinkoso.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel