Coronavirus: Wani sojan Najeriya ya kamu da cutar

Coronavirus: Wani sojan Najeriya ya kamu da cutar

- Wani jami'in sojan Najeriya ya kamu da cutar nan ta numfashi wacce aka fi sani da coronavirus

- Hedikwatar rundunar sojojin Najeriya ce ta tabbatar da hakan inda ta ce a yanzu haka yana asibiti yana jinya

- Jami'in sojan ya kasance matukin jirgin sama na yaki ne

Rahoto daga hedikwatar rundunar sojojin Najeriya ta tabbatar da cewar wani jami’in soja na kasar ya kamu da cutar coronavirus wacce ke ci gaba da yaduwa a fadin duniya.

Sojan, wanda ya kasance matukin jirgin sama na yaki ya koma kasar ne daga wani bulaguron da ya yi zuwa kasar waje, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Coronaviru: Wani sojan Najeriya ya kamu da cutar

Coronaviru: Wani sojan Najeriya ya kamu da cutar
Source: Twitter

Jami’in hulda da jama’a na cibiyar samar da bayanai a kan rundunoni na musamman a hedkwatar tsaro na kasar, Abdulssalam Sani ya bayyana cewa sojan na nan yana jinya a asibiti.

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Hukumar FAAN ta ce jiragen gida na aiki har yanzu

A wani labarin kuma, mun ji cewa Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Abba Kyari, wanda a ranar Talata, 24 ga watan Maris aka tabbatar da cewa yana dauke da cutar coronavirus ya isa cibiyar killacewa ta babban birnin tarayyar kasar nan Abuja.

Kyari a halin yanzu zai fara karbar magani da agajin likitocin Najeriya ne cibiyar.

Wata majiya da ta sanar da jaridar Daily Sun a kan cewa daya daga cikin na’urorin amfanin marasa lafiyan an kaishi fadar shugaban kasar don amfanin Abba Kyarin, ba gaskiya bane.

A kalamansa: “Zan iya tabbatar da cewa babu wata na’urar da aka fitar. Dukkansu suna nan. Dayan a sashin masu bukatar taimakon a koda yaushe na asibitin ne inda dayan ke cibiyar kebancewar.”

Kyari dai yayi tafiya ne zuwa kasar Jamus a ranar Asabar, 7 ga watan Maris inda ya hadu da jami’an Siemens a Munich don wani shirin fadada wutar lantarkin Najeriya. Ya dawo Najeriya kuwa a ranar Asabar, 14 ga watan Maris.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit.ng

Online view pixel