Yanzun-nan: Gwamnan Lagas ya rufe kasuwannin jahar

Yanzun-nan: Gwamnan Lagas ya rufe kasuwannin jahar

Gwamnan jahar Lagas, Babajide Sanwo-Olu, ya yi umurnin rufe kasuwanni da kantuna a jahar daga ranar Alhamis.

A cewarsa, lamarin bai shafi kasuwannin siyar da kayyakin bukata irin su kayayyakin magunguna, ruwa da kayan abinci.

Gwamnan a wani taron manema labarai a ranar Laraba ya ce: “ba za a rufe dukkanin harkoki bane, muna bukatar mutanen da ke siyar da kayayyakin bukata su tafi harkokinsu na yau da kullun.

Yanzun-nan: Gwamnan Lagas ya rufe kasuwannin jahar
Yanzun-nan: Gwamnan Lagas ya rufe kasuwannin jahar
Asali: Twitter

“Muna kokarin canja tsarin kasuwanni a Lagas. Wannan ne dalilin da yasa mike son amfani da wasu daga cikin rufaffun makarantunmu a matsayin kasuwanni, don mutane su samu damar siyan abinci da magani ba tare da su je wuri mai nisa ba.

“Sai kana da rai ne Za ka iya maganar tattalin arziki da kudi.”

A bangare guda mun ji cewa Gwamnatin jihar Legas ta bukaci duk wadanda suka halarci bikin shagalin African Magic Viewers’ Choice Award karo na 7 wanda aka yi a ranar 14 ga watan Maris 2020, su killace kansu don zai yuwu sun samu haduwa da mai cutar COVID-19.

Wannan na kunshe ne a wallafar da kwamishinan lafiya na jihar Legas, Farfesa Akin Abayomi yayi a twitter a ranar Talata, kamar yadda jaridar Daily Trust ta bayyana.

Kamar yadda jawabin ya bayyana, “Ina sanar da duk wadanda suka halarci bikin African Magic Viewers Choice Award wanda aka yi a ranar 14 ga watan Maris a Eko Hotels, a kan cewa zai yuwu sun ci karo da mai cutar coronavirus kuma akwai yuwuwar sun dauka cutar.”

KU KARANTA KUMA: Coronavirus: Hukumar FAAN ta ce jiragen gida na aiki har yanzu

Jaridar Daily Trust ta bayyana cewa, manyan mutane sun halarci wajen taron wadanda suka kunshi manyan ‘yan wasan kwaikwayo da manyan ‘yan jaridu.

A bikin an samu nishadantarwa daga manyan mawakan Afrika da suka hada da 2Baba Idibia, Osang Abang da kuma Cobhams, wanda yayi wakar ta’aziyyar manyan jaruman Nollywood da suka riga mu gidan gaskiya.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng