Coronavirus: Hukumar FAAN ta ce jiragen gida na aiki har yanzu
- Hukumar FAAN ta ce yan Najeriya a kasar na iya tafiya ba tare da matsala ba domin ba a dakatar da ayyukan jiragen gida ba
- Hukumar ta bayyana cewa haramcin da aka sanya wa dukkanin jiragen kasa da kasa saboda annobar coronaavirus bai shafi jiragen cikin gida ba
- Sai dai kuma FAAN ta bukaci dukkanin fasinjoji da sauran masu ruwa da tsaki da su bi dukkanin dokoki da ka’idoji domin ra’ayin kowa
Hkumar tashoshin jiragen sama na Najeriya (FAAN) ta bayyana cewa dukkanin yan Najeriya a kasar na iya tafiya ba tare da cikas ba domin ba a dakatar da ayyukan jiragen cikin gida ba.
Hukumar a wani jawabi da ta saki a ranar Talata, 24 ga watan Maris, ta bayyana cewa dukkanin haramcin da aka sanya kan jiragen kasa da kasa sakamakon anobar coronavirus bai shafi jiragen cikin gida ba.
Sai dai kuma FAAN ta bukaci dukkanin fasinjoji da sauran masu ruwa da tsaki da su bi dukkanin dokoki da ka’idoji domin ra’ayin kowa na gudun yadar cutar ta coronavirus a fadin kasar.
KU KARANTA KUMA: Yanzu-yanzu: Bayan fitowar sakamakon gwajinsa, Buhari ya shiga ganawa da hafsoshin tsaro
A wani labarin kuma, mun ji cewa gwamnan jihar Bauchi, Bala Mohammed Kauran Bauchi, ya kamu da cutar Coronavirus.
A wani jawabin da mai magana da yawun gwamnan, Muhktar M Gidado ya saki, ya tabbatar da rahoton inda ya bukaci alumma su taimakawa gwamnan da addu'o'i.
Jawabin yace “Muna sanar da daukacin jama'a cewa sakamakon gwajin mutane shida da cibiyar takaita yaduwar cututtuka ta gudanar kan gwamna Bala AbdulKadir Mohammed, iyalansa, da hadimansa da suka raka sa Legas ya fito.“
“Daga cikin sakamakon shida na mutum daya kadai ya tabbata ya kamu, kuma shine na Sanata Bala AbdulKadir Mohammed, gwamnan jihar Bauchi.“
“A yanzu haka, gwamnan ya killace kansa yayinda likitoci da maaiktakan hukumar sun dauki nauyin kula da shi.“
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng