Gwajin coronavirus: Buhari ya gana da Masari, ya shiga wata ganawar da shugabannin tsaro

Gwajin coronavirus: Buhari ya gana da Masari, ya shiga wata ganawar da shugabannin tsaro

Shugaban kasa, Muhammadu Buhari, ya yi wata ganawar sirri da Aminu Bello Masari, gwamnan jiharsa ta haihuwa, Katsina, a fadar gwamnatin tarayya da ke Abuja.

Ziyarar ta gwamna Masara na zuwa ne a cikin sa'o'i kadan bayan labarai sun gama zagayawa a kan cewa an yi wa shugaba Buhari gwajin kwayar cutar corona a ranar Litinin.

Wasu rahotanni da ba a tabbatar da su ba sun bayyana cewa ba a samu kwayar cutar a jikin shugaba Buhari ba, amma an same ta a jikin shugaban ma'aikatansa, Abba Kyari.

Gwamnan na jihar Katsina ya ki yin magana da manema labarai a fadar shugaban kasa bayan kammala ganawarsa da shugana Buhari.

Jim kadan bayan kammala ganawarsu, shugaba Buhari ya shiga wani taron da shugabannin hukumomin tsaro bayan tafiyar Masari.

Gwajin coronavirus: Buhari ya gana da Masari, ya shiga wata ganawar da shugabannin tsaro
Buhari da Masari
Asali: UGC

An ga shigar mai bawa shugaban kasa shwara a kan tsaro; manjo janar Babagana Monguno (mai ritaya), darektan hukumar tsaro ta farin kaya (DSS); Yusuf Magaji Bichi, da babban sifeton rundunar 'yan sandan Najeriya(IGP); Mohammed Adamu, ofishin shugaban kasa.

Legit.ng ta wallafa rahoton cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta yi amfani da sojoji da 'yan sanda wajen tabbatar da cewa jama'a sun nesanta da junansu domin takaita yaduwar kwayar cutar coronavirus.

DUBA WANNAN: COVID-19: El-Rufa'i ya umarci ma'aikatan jihar Kaduna su zauna a gidajensu, a rufe shaguna da kasuwanni

Ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawarsa da manema labarai a Abuja ranar Litinin.

A kuma yau, Talata, ne mazauna jihar legas suke ta tururuwar zuwa siyan takunkumin fuska da safar hannu a kasuwa don kare kai daga kamuwa da mugunyar cutar coronavirus.

Idan zamu tuna, ministan lafiya, Dr Osagie Ehanire ya yi barazanar sakin sunayen wadanda suka ki bin dokar killace kansu don taimakawa hana yada cutar a kasar nan.

Ehanire ya bada wannan sanarwar ne a ranar Litinin a Abuja yayin zantawa da manema labarai a kan halin da kasar nan ke cikin a kan annobar Covid-19.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel