Annobar Coronavirus: An Rufe dukkan kotunan Najeriya
Alkalin alkalan Najeriya, Tanko Mohammed ya umarci dakatar da dukkan zaman kotu a Najeriya, in banda na gaggawa, na tsawon kwanaki 14 sakamakon mugunyar cutar Covid-19.
Wannan sanarwar na kunshe ne a cikin takardar da alkalin alkalan ya fitar da yammacin ranar Litinin.
A umarnin da ya bayar makon da ya gabata, alkalin alkalan ya bada umarnin cewa duk mutumin da ba zai amince a duba lafiyarsa kafin shiga zauren kowacce kotu ba, toh ya koma gida.
An manna wannan sanarwar ne a kowacce kofar kotu inda aka bukaci dukkan ma’aikata da baki da suka hada da lauyoyi, ‘yan jarida da masu tsare lafiyar jama’a da su yi biyayya ga wannan dokar.
“Duk wanda ya ki biyayya, za a mayar dashi gida. Kiyayewa yafi magani,” takardar wacce jaridar Premium Times ta gani.
Wani likita da ke cikin kungiyar masana lafiyan da suke tantance jama’a a kofar kotun y ace, “Duk wanda aka samu dumin jikinsa ya zarta misali, za a mayar dashi gefe sannan a tambayesa a kan lafiyarsa”.
Legit.ng ta wallafa cewa gwamnatin tarayyar Najeriya ta ce za ta yi amfani da sojoji da 'yan sanda wajen tabbatar da cewa jama'a sun nesanta da junansu domin takaita yaduwar kwayar cutar coronavirus.
DUBA WANNAN: COVID-19: El-Rufa'i ya umarci ma'aikatan jihar Kaduna su zauna a gidajensu, a rufe shaguna a kasuwanni
Ministan yada labarai da al'adu na kasa, Lai Mohammed, ne ya sanar da hakan yayin wata ganawarsa da manema labarai a Abuja ranar Litinin.
Ministan ya ga baiken wasu jagorori da malaman addinai da suka yanke shawarar yin watsi da umarnin gwamnatin tarayya na hana taron jama'a masu yawa.
Wasu masallatai da coci-coci sun gudanar da taron ibada na ranar Juma'a da Lahadi kamar yadda suka saba duk da umarnin da gwamnati ta bayar na a rufe wuraren ibada a matsayin matakin dakile yaduwar kwayar cutar corona.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng