Coronavirus: Ku kawo mana dauki - Najeriya ta bukaci kasar Sin

Coronavirus: Ku kawo mana dauki - Najeriya ta bukaci kasar Sin

Ma'aikatar kiwon lafiyar Najeriya ta yi kira fa gwamnatin kasar Sin ta kawowa Najeriya dauki wajen yakar cutar Coronavirus a kasar bayan an samu mutane akalla 36 kuma daya ya mutu.

Ministan kiwon lafiya, Dakta Osagie Ehanire, ya mika wannan bukata ne yayinda jakadan kasar China zuwa Najerieya, Zhou Pingjian, ya kawo gudunmuwar kayayyakin aiki da magunguna ma'aikatar ranar Litinin a Abuja.

Ehanire ya yabawa gwamnatin kasar Sin kan namijin kokarin da sukayi wajen kawar da cutar a kasarsu yayinda mutane da al'ummar kasar suka koma rayuwarsu kamar bai faru ba.

Ya ce hanyoyin da kasar Sin tayi amfani da su wajen kawo karshen cutar zai zama abin koyi ga Najeriya wajen yakarta.

Saboda haka ya yi kira da gwamnatin kasar Sin ta taimakawa Najeriya da ma'aikata da zasu taimaka wajen shawo kan lamarin.

Ya ce Najeriya na bukatar daukar karatu wajen gwamnatin Sin kan yadda ta takaita yaduwar cutar.

Ehanire ya ce kasar na bukatar ma'aikata domin bibiyan mutane, na'urar numfashi, kayayyakin gwaji, da kuma kayan kariya ga ma'aikatan asibiti.

Jakadan Sin, Pingjian, ya bayyana cewa ba zasu manta irin goyon bayan da NAjerya ta nunawa kasarsu ba lokacin da suke fuskantar kalubalen.

Coronavirus: Ku kawo mana dauki - Najeriya ta bukaci kasar Sin

Coronavirus: Ku kawo mana dauki - Najeriya ta bukaci kasar Sin
Source: UGC

A bangare guda, An samu mutum na farko da ya mutu sakamakon kamuwa da cutar Coronavirus a Najeriya ranar Litinin, 23 ga Maris 2019.

Cibiyar takaita yaduwar cututtuka a Najeriya NCDC ta tabbatar da mutuwar a shafinta na Tuwita.

Jawabin ciyar yace “An samu mutuwar farko sakamakon COVID19 a Najeriya. Wani dan shekara 67 ne wanda ya dawo daga Ingila jinya.“

“Ya kasance mai fama da rashin lafiya da ciwon siga.“

Majiyarmu ta bayyana sunan mutumin matsayin, Suleiman Achigu wanda ya kasance tsohon dirakta manajan kamfanin kasuwancin man feturin Najerya PPMC.

Ya mutu misalin karfe 2 na dare a asibitin koyarwan jamiar Abuja.

Marigayin dan asalin jihar Kogi ne, kuma ya dawo daga Ingila makonni biyu da suka gabata.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Tags:
Online view pixel