Yanzun-nan: Gwamnan Zamfara ya bayar da umarnin rufe ko ina a jahar saboda coronavirus
- Gwamnan Zmfara, Muhammad Matawalle ya yi umurnin rufe duk wasu ofishoshi na gwamnati da ma’aikatu a fadin jahar
- Hakan na daga cikin matakin da gwamnatin jahar ta dauka domin hana yaduwar cutar coronavirus
- Bincike ya nuna cewa Gwamna Bello Muhammad ya kasance a cikin gida tun bayan da ya dawo jahar a ranar Alhamis da ya gabata daga wani tafiya da ya yi zuwa kasar waje
Gwamnatin jahar Zamfara ta rufe duk wasu ofishoshi na gwamnati da ma’aikatu a fadin jahar.
Bincike ya nuna cewa Gwamna Bello Muhammad ya kasance a cikin gida tun bayan da ya dawo jahar a ranar Alhamis da ya gabata daga wani tafiya da ya yi zuwa kasar waje bayan ya dan yada zango a Abuja.

Asali: UGC
Gwamnan ya halarci wajen duba cibiyar killace mutane na Coronavirus a cibiyar lafiya ta tarayya, Gusau a ranar Juma’a bayan ya dawo jahar.
Uwargidar gwamnan ta Hajiya Aisha Bello Muhammad ta soke wani taron manema labarai a gidan gwamnan da misalin karfe 3:00 na rana, sa’a daya kafin lokacin da aka shirya gudanar da taron.
Kwamishinan yan sandan jahar, Usman Nagoggo ya haramta duk wani taro a fadin kasar sannan ya yi umurnin rage yawan mutane a ofishishin yan sanda, ciki harda sallaman dukkanin masu kananan laifuffuka.
KU KARANTA KUMA: An samu karin sabbin alamomi dake bayyanar da Coronavirus a jikin dan Adam
A wani labari makamancin haka mun ji cewa Gwamnan jahar Neja, Alhaji Abubakar Sani Bello ya sanar da rufe harkoki a jahar, inda ya kaddamar da hana zirga-zirga daga karfe 8:00 na safe zuwa 8:00 na dare.
A cewar gwamnan takaita zirga-zirgan zai fara ne daga ranar Laraba kamar yadda ya sanar a ranar Litinin, 23 ya watan Maris.
Ya ce akwai bukatar daukar wannan mataki sakamakon sabbin mutanen da aka samu sun kamu da cutar Coronavirus a Abuja, wanda jahar Neja ce mafi kusa da birnin tarayyar.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng