Sanusi ya bukaci masu kai masa ziyara su dakata saboda barkewar Coronavirus

Sanusi ya bukaci masu kai masa ziyara su dakata saboda barkewar Coronavirus

Yayin da cutar nan ta Coronavirus ta ke cigaba da bulla a wurare daban-daban har a Najeriya, Muhammadu Sanusi II ya fito ya yi wa jama’a jawabi na musamman.

A wani bidiyo da ya shigo hannun Legit.ng Hausa, Malam Muhammadu Sanusi II ya nuna godiya ga dinbin Masoyan da su ke cigaba da kai masa ziyara a wannan lokaci.

Tsohon Mai martaban ya bayyana cewa Bayin Allah daga cikin gida da wajen Najeriya sun yi ta kawo masa ziyara domin nuna goyon bayansu tare da yi masa addu’o’i.

Mai martaba Muhammadu Sanusi II ya ja-kunnen Jama’a game da annobar COVID-19, don haka ya bukaci Masoyan na sa da su tsaida kawo masa ziyara a wannan yanayi.

Sanusi II ya nemi masu taya sa alhini da nuna kauna da su jinkirta ziyarar da su ke kawowa har sai zuwa lokacin da wannan cuta ta lafa, kamar yadda Masana su ke gargadi.

KU KARANTA: Coronavirus ta shigo Najeriya amma Shugaba Buhari bai ce uffan ba

A cewar tsohon Sarki Sanusi II, akwai bukatar mutane su dakatar da duk wata zirga-zirga da ba ta zama dole ba, domin akwai yiwuwar kamuwa da cutar a jirgin sama ko mota.

Ganin cewa ana saurin kamuwa da cutar a wajen tafiye-tafiye, Muhammadu Sanusi II ya nemi dinbin Masu kauna su bi matakan da aka kawo na rage balaguro da yawo.

Malam Sanusi II ya nuna cewa muddin wannan cuta ta lafa, a shirya ya ke ya cigaba da karbar masu kawo masa ziyara, kamar yadda ya saba tun bayan cire masa rawani.

A jawabin na sa, tsohon gwamnan babban bankin ya yi kira ga mutane su saurari shawarwarin da hukuma su ka bada na wanke hannu domin hana yaduwar wannan cutar.

Bayan haka tsohon Sarkin ya bada shawara ga duk wadanda su ka fuskanci wasu alamu na wannan cuta da su ruga asibiti. A karshe ya yi addu’ar waraka daga COVID-19.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel