Ronaldinho ya koyi sana’ar kafinta a gidan yarin kasar Paraguay
Yayin da ake cigaba da tsare Ronaldo de Assis Moreira watau Ronaldinho a gidan kurkuku a kasar Paraguay, mun samu labari cewa ya koyi sana’ar hannu.
Tsohon ‘Dan wasan na kungiyar Barcelona da ya fi shahara da Gaucho Ronaldinho ya koyi aikin kafinta tare da sauran mutanen da ya ke tare da su a kurkuku.
Ronaldinho ya koyi wannan sana’a ne jim kadan bayan ya jagoranci gasar kwallon da aka shirya da sauran wadanda ke tsare a gidan yari tare da shi a yanzu.
Bayan aikin kafinta, Ronaldinho ya kan buga kwallon kafa, inda a wani wasa ya zura kwallaye biyar a raga, sannan kuma ya taimaka wajen cin wasu kwallaye.
Wani ‘Dan wasan Paraguay, Fernando Lugo, ya shaidawa ‘Yan jarida cewa ya samu Ronaldinho a gidan yari cike da murmushi kamar yadda dai kowa ya san shi.
KU KARANTA: Ronaldinho ya shafe darensa na farko a kurkukun kasar Paraguay
A kan koyawa wadanda ke zaman kaso sana’a ta yadda za su dogara da kansu a lokacin da su ka fito daga gidajen kurkuku domin su rike hanyar samun kudi.
Ba a bar tsohon Tauraro Ronaldinho a baya ba, wanda yanzu Mahukuntar kasar Amurkan su ka yi ram da shi bayan an same shi dauke da takardun fasfo na bogi.
Tsohon ‘Dan kwallon na Brazil zai iya shafe watanni shida a gidan kason, don haka ya shiga cikin sahun wadanda ake koyawa aikin kafinta inji Jaridar Pulse.
Yanzu haka Ronaldinho ya na jiran ranar da Alkali zai yanke masa hukunci. Ana zargin cewa za a gurfanar da Tauraron har da laifin safarar makudan kudi.
Idan ba ku manta ba, Ronaldinho ya yi bikin cika shekaru 40 a Duniya ne a cikin wannan gidan yari. Abokan zamansa sun shirya masa biki a wannan rana.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng