Coronavirus: Tattalin arzikin duniya zai shiga garari na tsawon shekaru - Kungiya

Coronavirus: Tattalin arzikin duniya zai shiga garari na tsawon shekaru - Kungiya

- Kungiyar bunkasa tattalin arziki da ci gaba ta kasashen duniya ta yi jan kunne cewa za a dauki shekaru masu tsawo kafin a iya farfadowa daga annobar coronavirus

- Sakatare janar na kungiyar, Angel Gurría, ya bayyana cewa tabarbarewar da tattalin arzikin ke ciki ya zarce na wanda ake tunanin shiga

- Ya yi kira ga gwamnatoci su tanadi wasu dokoki na kashe kudi don tabbatar da cewa an magance wannan cuta

Rahotanni sun kawo cewa kungiyar bunkasa tattalin arziki da ci gaba ta kasashen duniya wato OECD ta yi jan kunne cewa za a dauki shekaru masu tsawo kafin a iya farfadowa daga annobar coronavirus.

Sakatare janar na kungiyar, Angel Gurría, ya bayyana cewa tabarbarewar da tattalin arzikin ke ciki ya zarce na wanda ake tunanin shiga, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Coronavirus: Tattalin arzikin duniya zai shiga garari na tsawon shekaru - Kungiya
Coronavirus: Tattalin arzikin duniya zai shiga garari na tsawon shekaru - Kungiya
Asali: Facebook

Ya bayyana cewa Allah ne kawai zai sa a yi amannar cewa kasashe za su farfado nan kusa daga halin da aka fada.

Kungiyar ta OECD ta yi kira ga gwamnatoci su tanadi wasu dokoki na kashe kudi don tabbatar da cewa an magance wannan cuta.

KU KARANTA KUMA: An samu karin sabbin alamomi dake bayyanar da Coronavirus a jikin dan Adam

A bangare guda kuma mun ji cewa shekaru kafin barkewar mugunyar cutar coronavirus da ta lashe rayukan jama'a a duniya, babban hamshakin mai kudi Bill Gates ya ja kunnen duniya a kan a dage da tarbar mummunan kalubalen cuta a fadin duniya.

Gates ya sanar da hakan ne a yayin tsokaci a jawabin da aka yi na Massachusetts Medical Society a Boston a watan Afirilu na 2018.

A yayin da yake tsokaci a kan kokarin masu bincike a kan magungunan HIV, zazzabin cizon sauro da Polio, babban mai kudin yayi hasashen irin abinda ke tunkaro duniya.

"Akwai wani bangare daya da duniya bata samun ci gaba, shine shirya tarar annoba," Gates yace.

"Ya kamata wannan ya zama abinda ya damemu gaba daya, saboda idan tarihi ya koya mana darasi, zamu gane cewa za a iya samun barkewar annoba a duniya." ya kara da cewa.

Ya shawarci cewa a habaka wasu bangarori. "Abinda duniya ke bukata sannan muke bukata don kariya a garemu shine makamai da kuma hanyar shawo kan annoba da gaggawa."

Mashahurin mai arzikin ya kara da cewa idan annobar 1918 ta sake dawowa a yau, kusan mutane miliyan 33 na duniya ne zasu mutu a cikin watanni shida kacal.

Kamar yadda yace, gidauniyarsa na kokarin habaka wani riga-kafi na kowacce irin cuta a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel