Gwaji ya nuna Cavaye Yeguie ya na da cutar COVID-19 a Kamaru
Rahotanni su na zuwa mana daga Jaridar kasar waje ta 237 Online cewa shugaban majalisar tarayyar kasar Kamaru, Cavaye Yeguie, ya kamu da cutar COVID-19.
Halin ko-in-kula da kunnen kashin Honarabul Cavaye Yeguie Djibril ne su ka yi sanadiyyar da ya kamu da wannan cuta kamar yadda rahotannin jaridar su ka bayyana.
Ana rade-radin cewa Mai girma Cavaye Yeguie Djibril ya yi watsi da dokokin da matakan kiwon lafiya da aka gindaya a lokacin da ya yi wata tafiya zuwa kasar waje.
Bayanan da su ke fitowa daga asibiti sun bayyana cewa Cavaye Djibril bai bi matakan gujewa kamuwa da wannan cuta ba a lokacin da ya ke filin jirgin saman kasar.
Hukumomin Kamaru sun ja kunne da cewa bin jirgin Air France ta babban filin tashi da saukar jirgin sama na Yaoundé Nsimalen ya na hadari, amma wasu su ka ki ji.
KU KARANTA: Cikakken Jerin Jihohin da cutar Coronovirus ta ratsa a Najeriya
Cavaye Yeguie Djibril ya na cikin wadanda su ka yi kememe su ka yi tafiya ta wannan jirgi. Yanzu dai Ministan lafiyan kasar ya bukaci a killace duk fasinjojin da su ka bi jirgin.
Saboda gudun a killace shi a asibiti, Cavaye Yeguie Djibril ya ruga majalisar tarayya. Ana tsoron cewa wannan abu da ya yi, ya jefa lafiyar ‘yan majalisar kasar a cikin hadari.
Shugaban majalisa Cavaye Yeguie Djibril ya jagoranci duka zaman da majalisar Kamaru ta yi duk da ya na dauke da cutar. Hakan na iya sa Abokan aikinsa su kamu da COVID-19.
Bisa dukkan alamu, ma’aikatar lafiya za ta bukaci a killace daukacin ‘Yan majalisar da aka yi zaman da su. Wannan zai taimaka wajen dakile yaduwar muguwar cutar.
Sai dai duk da haka kasar ta na cikin barazana a halin yanzu domin zai yi wahala a iya tattaro wadanda su ka yi mu’amala da ‘Yan majalisar kasar a ‘yan kwanakin nan.
Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:
https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.
Asali: Legit.ng