Coronavirus: Mutanen da suka mutu a Faransa sun kai 674

Coronavirus: Mutanen da suka mutu a Faransa sun kai 674

- Cutar coronavirus ta kashe mutane 674 a kasar faransa

- Hakan ya biyo bayan rahoton mutane 112 da aka tabbatar da mutuwarsu cikin sa’a 24 da ta gabata

- An tattaro cewa yawan mutane 16,018 ne suka kamu da cutar a kasar ta Faransa

Rahotanni sun kawo cewa akalla mutane 674 ne suka mutu a kasar Faransa sakamakon cutar coronavirus bayan an bayar da rahoton mutane 112 da aka tabbatar da mutuwarsu cikin sa’a 24 da ta gabata.

Wani jami’in hukumar Lafiya, Jerome Salomon a ranar Lahadi, 22 ga watan Maris, ya bayyana cewa cutar ta kashe sannan tana ci gaba da yin kisa.

Coronavirus: Mutanen da suka mutu a Faransa sun kai 674

Coronavirus: Mutanen da suka mutu a Faransa sun kai 674
Source: Twitter

Jumullar mutane 16,018 ne suka kamu da cutar a kasar ta Faransa, sai dai Mista Salomon ya ce wasu na ganin adadin mutanen ya fi haka.

Gwamnati ta hana zirga-zirga tun daga ranar Talata sai dai fa mai matukar muhummanci.

Mista Salomon ya shawarci mutane da su "kara hakuri".

KU KARANTA KUMA: Ku zauna a gida: Gwamnatin jihar Legas ta bawa dukkan ma'aikatanta hutu saboda coronavirus

A wani labarin kuma mun ji cewa bayan kara samun karuwar mutane a kalla 19 da suka kamu da kwayar cutar corona a kasar Saudiyya, shugaban masallatan Haramain da ke birnin Makkah da Madinah, Sheikh Sudais, ya bayar da umarnin a nade shinfidun da ke cikin masallatan.

A wata sanarwa da shafin masallatan ya fitar a shafinsa na dandalin sada zumuntar 'facebook' (Haramain Sharifain), an bayyana cewa za an maye gurbin kafet din masallatan da wasu layuka da aka zana a kan tayil din masallatan.

A sanarwar da aka wallafa a shafin, an ga hotunan wasu ma'aikatan masallatan na nade kafet din tare da zana sabbin layukan.

Nade shimfidun masallatan na daga cikin matakan kiyaye wa da kare yaduwar kwayar cutar coronavirus da ke cigaba da yaduwa a sassan duniya.

A cikin makon jiya ne hukumomin kasar Saudiyya suka sanar da rufe masallatan Harami da dakatar da aikin Umrah sakamakon bular annobar kwayar cutar corona.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel