Coronavirus: Ganduje ya bayar da umarnin rufe makarantun Islamiyya da na allo

Coronavirus: Ganduje ya bayar da umarnin rufe makarantun Islamiyya da na allo

Gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rufe dukkan makarantun boko, Islamiyya da na allo daga ranar Litinin, 23 ga wata, domin hana yaduwar kwayar cutar coronavirus da ta addabi duniya.

Shugaban makarantun Qur'ani, Islamiyya da Tsangaya, Sheikh Yahuza Gwani Dan Zarga, ya tabbatar da rufe makarantun ga manema labarai ranar Lahadi a Kano.

A cewarsa, umarnin rufe makarantun ya biyo bayan shawarar da gwamnonin jihohin arewa ta yamma suka yanke na rufe dukkan makarantu domin takaita haduwar mutane wuri saboda dakile yaduwar kwayar cutar coronavirus.

"Ana umartar dukkan makarantun Qur'ani, Islamiyya da Tsangaya a kan su rufe makarantu daga ranar Litinin, 23 ga watan Maris, kamar yadda gwamnatin jiha ta umarta," a cewarsa.

Coronavirus: Ganduje ya bayar da umarnin rufe makarantun Islamiyya da na allo

Gwamna Ganduje
Source: Facebook

Gwani Yahuza ya ce bayar da umarnin rufe makarantun tsangaya guda 12 da ke jihar Kano ba yana nufin dakatar da harkokin koyarwa bane, an dauki matakin ne domin kare jama'a daga kamuwa da kwayar cutar COVID-19.

DUBA WANNAN: Coronavirus: Jawabin shugaba Buhari ga 'yan Najeriya (Bidiyo)

"Mu na kira ga shugabannin addini da sauran jagorori a kan su tashi tsaye da addu'o'i domin neman taimakon Allah wajen kawo karshen annobar coronavirus," a cewar Gwani Yahuza.

A ranar Juma'a ne gwamnatin jihar Kano ta bayar da umarnin rufe dukkan kanana da manyan makarantunta na tsawon kwanaki 30 saboda annobar kwayar cutar coronavirus. Sai dai, jama'a da dama na tunanin cewa umarnin bai shafi makarantun Qur'ani, Islamiyya da Tsangaya ba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Online view pixel