Babu coronavirus a Jami'ar Bayero - Hukumar Jami'ar

Babu coronavirus a Jami'ar Bayero - Hukumar Jami'ar

Hukumar Jami'ar Bayero da ke jahar Kano ta bayyana cewa gaskiya ba ne labarin da aka rika yadawa cewa an samu bullar cutar coronavirus a jami'ar.

A yau Lahadi ne dai aka fara yada wani labari da ke cewa Ma'aikatar Lafiya ta Jihar Kano ta tabbatar da wasu dalibai biyu sun kamu da annobar coronavirus a Jami'ar Bayero.

A wata hira da Shugaban Jami'ar, Farfesa Muhammad Yahuza ya ce labarin ba komai bane face karya sannan ya ce babu ma dalibai a dakunan kwanan jami'ar, shafin BBC Hausa ta ruwaito.

Babu coronavirus a Jami'ar Bayero - Hukumar Jami'ar

Babu coronavirus a Jami'ar Bayero - Hukumar Jami'ar
Source: UGC

Ya ce "Wannan labari ba shi da tushe ballanta makama. An dauki hoton boge ne na shafi mai sunan BBC ana yadawa domin a nuna kamar daga BBC yake.

"A halin da ake ciki ma babu dalibai a dakin kwana na Jami'ar Bayero. Kamar yadda aka sani an yi yajin aiki na sati biyu. Kafin haka kuma dalibanmu suna hutun tsakiyar zango. Mun bayar da hutun mako daya sai kuma aka tafi yajin aikin."

Farfesa Yahuza ya kuma yi Allah-wadai da wadanda suka kirkiri labarin karyar sannan ya yi kira ga masu yadawa da su guji yin hakan.

KU KARANTA KUMA: Allah ya yi min wahayi game da cutar coronavirus – Babban Fasto

A wani labarin kuma mun ji cewa Gwamnatin jihar Legas ta bawa dukkan ma'aikatanta; daga kan mataki na daya zuwa na 12, umarnin su zauna a gida na tsawon kwanaki 14 masu zuwa.

Gwamnan jihar Legas, Babajide Sanwo Olu, ne ya sanar da hakan yayin da yake gabatar da karin jawabi a kan bullar annobar kwayar cutar corona a jiharsa ranar Lahadi. Ya bayyana cewa ma'aikatan zasu cigaba da zama a gida ne na tsawon kwanaki 14 masu zuwa.

A cikin makon da muka yi bankwana da shine gwamnatin jihar Legas ta bayar da umarni rufe dukkan makarantu da wuraren ibada da ke jihar.

Hakan na zuwa ne a daidai lokacin da adadin masu kamuwa da kwayar cutar corona ke karuwa a jihar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel