Coronavirus: Hanyoyi 4 da mutum zai bi don kare kai daga cutar

Coronavirus: Hanyoyi 4 da mutum zai bi don kare kai daga cutar

Hukumar lafiya ta duniya wato WHO ta wallafa matakan da mutum zai bi don kare kai daga kamuwa da annobar Coronavirus da ya karade duniya.

Cutar dai kan sa mutum ya fuskanci kalubale wajen jan numfashi.

Coronavirus: Hanyoyi 4 da mutum zai bi don kare kai daga cutar

Coronavirus: Hanyoyi 4 da mutum zai bi don kare kai daga cutar
Source: Facebook

Ga matakan da hukumar ya lissafa kamar haka:

1. Mutum ya lazumci wanke hannayensa da sabulun gargajiya ko sabulun wanke hannu na ruwa, wanda zka iya kashe kwayoyin cuta

2. Mutum ya dunga rufe hanci da bakinsa lokacin da yake yin atishawa da kyallen fyace majina sannan yawanke hannayensa bayanya yi atishawa domin hana kwayoyin cutar yaduwa.

3. Mutum ya guji taba idanunsa, ko hanci ko bakinsa, idan kuma hannunsa ya taba wurin da cutar ta shafa, za ta iya yaduwa zuwa sauran sassan jikinsa.

4. Kada a rika matsawa kusa da mutanen da ke yawan atishawa ko tari da masu fama da zazzabi, za su iya watsa cutar cikin iska ta yadda ku ma za ku iya kamuwa da ita. Akalla a matsa nesa da su ta yadda tazarar da ke tsakani za ta kai kafa uku.

A wani labarin kuma, mun ji cewa jahar Oyo ta samu mutum na farko da ya kamu da cutar Coronavirus, inda hakan ya zama lamari na 23 da aka samu a Najeriya.

Akwai wadanda suka kamu mutum 16 a Lagas; daya a Ekiti; biyu a Ogun sannan uku a babbar birnin tarayya Abuja.

A wani jawabi da aka saki a safiyar ranar Lahadi, Seyi Makinde, gwamnan Oyo, ya ce jami’an hukumar lafiya a jahar suna hada kai da asibitin jami’ar jahar da tawagar Ibadan kan lamarin.

Gwamnan ya kara da cewa an killace wani da ya dawo daga kasar Amurka kwanan nan.

“Gwajin COVID-19 da aka yi wa wani a Bodija ya dawo cewa yana dauke da cutar. An saki sakamakon gwajin da misalin karfe 5:35 na yammacin ranar Asabar, 21 ga watan Maris,” in ji shi.

Gwamnan ya saki jerin layukan da za a kira domin agaji kamar haka: 08038210122/ 08023228267/ 08073431342.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel